Labarai
BUK Ta Musanta Zarge-Zargen Cin Hanci Kan Tsohon Shugaban Sashen Kula Da Ɗalibai
Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK) ta musanta zarge-zargen cin hanci da aka yi wa tsohon Shugaban Sashen kula da Harkokin Ɗalibai, Farfesa Shamsuddeen Umar, tana mai bayyana zargin a matsayin ƙarya, marar tushe kuma na ɓata suna.
Matsayar jami’ar na kunshe cikin wata sanarwa da Shugaban Sashen Kafofin Sadarwa na Dijital, Nura Garba, ya fitar a madadin Magatakardar jami’ar, sakamakon wani rubutu da Mr. Abdulrahman Abdulateef, wanda aka fi sani da MC Almajiri, tsohon ɗalibi a Sashen Ilimin Ƙasa (Geology), ya wallafa a kafafen sada zumunta.
A cewar sanarwar, jami’ar ta yi watsi da zarge-zargen baki ɗaya, tana mai jaddada cewa Farfesa Umar ya yi wa jami’ar hidima cikin kwarewa, gaskiya da ƙwarewar aiki tsawon lokacin da ya rike muƙaminsa.
Jami’ar ta bayyana cewa an tsawaita wa’adin naɗin Farfesa Umar a matsayin Dekan Harkokin Ɗalibai sau da dama, sakamakon kyakkyawan aikinsa da jajircewarsa wajen kula da walwalar ɗalibai da al’ummar jami’a gaba ɗaya.
BUK ta ƙara da cewa babu wani tarihin aikata ba daidai ba ko cin hanci da aka taɓa samu a kansa yayin gudanar da aikinsa na hukuma.
Sanarwar ta ce: “Jami’ar na kallon wannan wallafa a matsayin yunkuri na gangan domin ɓata sunan jami’a da kuma ɗaya daga cikin manyan jami’anta masu mutunci.”
Saboda haka, jami’ar ta buƙaci Abdulateef da ya gaggauta janye waɗannan zarge-zargen na ɓata suna tare da ba da haƙuri a bainar jama’a ga jami’ar da kuma Farfesa Umar.
Jami’ar ta kuma yi gargaɗin cewa rashin bin wannan buƙata zai tilasta mata ɗaukar matakin shari’a da ya dace domin kare martabarta da kuma sunan ma’aikatanta.
A ƙarshe, jami’ar ta jaddada ƙudurin ta na ci gaba da kiyaye mafi girman matakan ɗabi’a, gaskiya da ƙwarewar ilimi, tana mai cewa ba za ta lamunci duk wani aiki da zai iya raunana ƙimarta da martabarta ba.
Khadijah Aliyu
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
