Connect with us

Labarai

BUK Ta Shirya Taro Kan Inganta Harkokin Kudi A Aikin Gwamnati

Published

on

Jami’ar Bayero Kano (BUK) ta sake jaddada kudirinta na ci gaba da samar da sauye-sauyen zamani wajen tafiyar da  harkokin kuɗi a aikin gwamnati a Najeriya da sauran kasashen Afirka.

Shugaban jami’ar, Farfesa Haruna Musa ne ya bayyana wannan kudirin a taron ƙasa da ƙasa na farko kan harkokin mulkin jama’a, wanda sashen gudanarwa na jama’a, karkashin tsangayar nazarin harkokin tattalin arziki ta shirya.

Shugaban, wanda Mataimakiyar Shugaban Jami’a mai kula da Bincike da Cigaba, Farfesa Amina Mustapha ta wakilta, ya jaddada cewa BUK na kan gaba wajen jagorantar harkokin ilimi da suka dace da muradun ‘yan ƙasa bisa ƙa’idojin duniya.

Ya bayyana taken taron a matsayin abin da ya dace a wannan lokaci, tare da yin kira ga mahalarta da su yi amfani da ilimin da suka samu domin inganta tsarin mulki a Najeriya da Afirka.

A cikin saƙon fatan alheri, shugaban taron kuma Shugaban Hukumar Bincike da Cigaban Ilimin Najeriya (NERDC), Farfesa Salisu Shehu, ya jaddada canjin gaggawa da tattalin arzikin zamani ya haifar.

Ya ce Afirka na fuskantar sauye-sauye masu ban mamaki, kuma irin waɗannan taruka na zama tamkar ƙarfafa ingantaccen mulki da gaskiya ne a harkokin kudi.

Mai gabatar da muƙalar farko, Matawallen Zazzau kuma malami a Jami’ar Kaduna, wanda shi ne shugaban Hukumar Kula da Ma’aikatan Kananan Hukumomin Jihar Kaduna, Farfesa Aminu Ladan Sharehu, ya bayyana hanyoyin da Afirka musamman Najeriya za ta iya sauya manufofin jama’a da tsarin kuɗi domin haɓaka cigaba mai ɗorewa.

Ya lura cewa taron ya mai da hankali ne wajen nazarin yadda za a iya amfani da manufofin jama’a da tsarin kuɗi wajen inganta mulki mai nagarta.

Ɗaya daga cikin mahalarta taron, Mataimakin Daraktan Gudanarwa na Ƙaramar Hukumar Sabon Garin Jihar Kaduna, Nura Ibrahim Aminu, ya bayyana muhimmancin shirye-shiryen da al’umma suka jagoranta da kuma tarurrukan tattaunawa a yankuna wajen inganta gaskiya da cigaban ƙasa daga tushe.

Taron, na yini uku, mai taken “Sauya Manufofin Jama’a, Harkokin Kuɗi da Gudanarwa Domin Cigaba mai Ɗorewa a Afirka: Matsaloli, Kalubale da Hanyoyin Magance Su” ya samu  mahalarta masana da dama daga ciki da wajen ƙasa.

 

Daga Khadijah Aliyu

Labarai

Labarai15 hours ago

Tinubu Ya Yi Jimamin Rasuwar Bamanga Tukur

Daga Bello Wakili  Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana alhininsa kan rasuwar dattijo, ɗan kasuwa kuma tsohon Gwamnan tsohuwar...

Labarai23 hours ago

Hukumar Alhazai ta Jigawa Ta Nemi Karin Kujerun Hajji na 2027

Jigawa, HuUsman Muhammad Zaria  Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta nemi karin kujerun aikin Hajjin 2027 daga Hukumar...

Labarai3 months ago

Kungiyar Zabi Sonka Reshen Kaduna Ta Kaddamar Da Kalandar Shekara

A kokarin ganin an kara karfafa dankon zumunci a tsakanin al’ummar tarayyar Najeriya da kuma jama’ar wadansu kasashe kungiyar Zabi...

Labarai3 months ago

Gwamna Namadi Ya Taya Najeriya Murnar Ranar Dimokuraɗiyya

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya taya al’ummar Najeriya da mazauna jihar murnar Ranar Dimokuraɗiyya...

Labarai3 months ago

EU Ta Ƙara Azama Wajen Tallafa Wa Arewacin Najeriya

Wata babbar tawaga ta shugabannin ofisoshin ƙasashen Tarayyar Turai (EU) da mataimakansu ƙarƙashin jagorancin Jakadan EU a Najeriya da ECOWAS,...

Labarai3 months ago

Kano: CDA Ta Raba Tan 2.85 Na Ingantattun Iri

Daga Khadijah Aliyu  Cibiyar bincike kan inganta noma a yankunan da ke da ƙarancin ruwa ta Jami’ar Bayero Kano(CDA), ta...

Labarai3 months ago

Jigawa Ta Ware Naira Miliyan 835 Don Sayen Kayan Agajin Gaggawa Saboda Ambaliya

Daga Usman Muhammad Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da sayen kayayyakin agajin gaggawa na shirin tunkarar ambaliya da mayar da...

Labarai3 months ago

Jami’an Tsaro Sun yi Nasarar Hallaka ‘Yan Bindiga 6 a Zamfara

Daga Aminu Dalhatu Rundunar ’Yan Sanda a Jihar Zamfara tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro sun yi nasarar dakile...

Labarai3 months ago

Gwamnatin Jigawa Ta Amince da Ƙarin Ayyuka Kan Ginin Hedikwatar Injinan Noma

Daga Usman Muhammad Zaria Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da ƙarin ayyuka na ginin hedikwatar Kamfanin Injinan Noma...

Kasuwanci3 months ago

Gwamnatin Jigawa Ta Amince da Sakin Kuɗaɗe Domin Gudanar da Taron Zuba Jari na 2026

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce ta amince da sakin kuɗaɗen da aka riga aka ware wa...

Mafi Shahara