Labarai
Tinubu Ya Nada Lamido Yuguda Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Kasa
Daga Bello Wakili
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada Lamido Abubakar Yuguda a matsayin Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Kasa CBN, wanda ake sa ran Majalisar Dattijai za ta tabbatar da shi.
Nominaciyar tana bisa tanadin Sashe na 8, sakin layi na 1 na Dokar Central Bank of Nigeria Act 2007.
Nadin Yuguda ya biyo bayan nadin tsohon Mataimakin Gwamnan, Bala Bello, a matsayin Mashawarci na Musamman ga Shugaban Kasa kan Harkokin Tattalin Arziki.
Shugaba Tinubu ya bukaci Yuguda da sauran jami’an bankin da su gudanar da ayyukansu bisa jajircewa, ƙwarewa, da sadaukarwa, domin tabbatar da daidaiton tattalin arziki da ci gaban kasa.
Lamido Yuguda ya taba rike mukamin slShugaban Hukumar Kasuwannin Hannun Jari daga shekarar 2020 zuwa 2024.
Ya samu digiri na farko a fannin Lissafi na Kasuwanci (Accountancy) aa Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a shekarar 1983, sannan daga baya ya samu digiri na biyu a fannin Kudi, wato Banking and Finance daga Jami’ar Birmingham a shekarar 1991.
Yuguda memba ne a Cibiyar Ƙwararrun Masu Lissafi ta Najeriya (ICAN) kuma Ƙwararren Masanin Kudi.
Ya fara aikinsa a CBN a shekarar 1984 a matsayin Babban Mai Kula da Ayyuka a Sashen Harkokin Kudi na kasashen Waje.
Daga baya ya yi aiki a matsayin masanin tattalin arziki a sashen Afrika a Asusun Bada Lamuni na Duniya daga shekarar 1997 zuwa 2001 kafin ya koma CBN.
Ya yi ritaya daga CBN a shekarar 2016 bayan ya shugabanci Sashen Gudanar da Ajiyar Kudi na tsawon shekaru shida.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
