Labaran Gida
Taiwo Oyedele Zai Maye Gurbin Minista a Ma’aikatar Kudi
Daga Bashir Meyere
Majalisar Dattawa ta tabbatar da naɗin Mista Taiwo Oyedele a matsayin Ministan kasa,.
Kafin nadin nasa, Mista Taiwo ya kasance Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan dokokin gyaran haraji, inda ya taka rawar gani wajen jagorantar dokokin gyaran haraji da Majalisar Tarayya ta amince da su, sannan Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya rattaba hannu a kansu.
Tabbatar da naɗin nasa ya biyo bayan sa’o’i na tambayoyi masu zurfi daga sanatoci daga jam’iyyun siyasa daban-daban, kan batutuwan tsaro, tattalin arziki da harkokin kuɗi da suka shafi ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin ‘yan Najeriya.
Yayin da yake amsa wasu daga cikin tambayoyin, Taiwo Oyedele ya bayyana cewa sayar da ɗanyen mai na iya taimakawa wajen ƙarfafa tattalin arziki, daidaita kudaden shiga na gwamnati, tare da samar da daidaitaccen farashin man fetur a ƙasar.
Ya ƙara da cewa idan aka kayyade farashi na wani kaso na ɗanyen man Najeriya na wani lokaci, gwamnati za ta iya tabbatar da samun kasafin kuɗi tare da rage tasirin sauyin farashin mai a kasuwannin duniya.
Dangane da matsalar rashin biyan kuɗin ‘yan kwangila saboda ƙarancin kuɗaɗen shiga, Oyedele ya ba da shawarar cewa a rika ba da kwangiloli ne gwargwadon kuɗin da ake da su domin kauce wa taruwar matsalolin biyan kuɗin da sauransu.
Ya bayyana cewa irin wannan yanayi na iya sa kwangilar da aka fara da farashin naira biliyan ɗaya ta tashi zuwa naira biliyan biyu, domin rufe asarar da ‘yan kwangila ke yi sakamakon jinkirin biyan su daga gwamnati.
Game da hanyoyin samun kuɗaɗen shiga na ƙasar, Oyedele ya ce an fi mayar da hankali kan harajin man fetur da iskar gas, yayin da sauran fannoni kamar ma’adinai ke da babbar dama ta samar da kuɗaɗen shiga, amma ba a ba su kulawa yadda ya kamata ba.
Oyedele ya jaddada buƙatar yin sahihin kasafin kuɗi tare da aiwatar da ayyukan da aka amince da su yadda ya kamata. Ya ce idan aka yi kasafin kuɗi, dole ne a tabbatar da cewa akwai kuɗin da za a aiwatar da shi, tare da sakin kuɗaɗe domin a kammala ayyukan musamman na ababen more rayuwa.
A jawabin sa bayan tabbatar da naɗi, Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya yabawa Shugaba Bola Tinubu kan naɗin Oyedele, yana mai cewa mutum ne mai ƙwarewa kuma ya dace da wannan muƙami.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
