Labarai
Tabbatar kana ganin likita akai-akai Don Hana Makanta – Dr. Avar

Dokta Gideon Avar, likitan ido, ya jaddada mahimmancin duba lafiyar mutanen da suka kai shekaru arba’in zuwa sama don hana makanta.
Kamar yadda Daraktan Likitoci na Cibiyar Ido ta Nobis da ke Jalingo, Jihar Taraba, Dokta Avar ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a asibitin ido na Nobis VIP da ke mil 6.
Duk da kalubalen da asibitinsa ke fuskanta, Dokta Avar ya ambata cewa suna sadaukarwa don taimaka wa majiyyata ta hanyar rage farashin kuɗin magani.
Ya bayyana cewa galibin ayyukan da suke yi na aikin agaji ne, kuma a wani bangare na ayyukansu na zamantakewar al’umma, sun samar da rijiyoyin burtsatse guda hudu a cikin al’ummar da suke zaune domin samar da ruwan sha kyauta ga mutane.
Dokta Avar ya bukaci daidaikun mutane, musamman wadanda suka haura shekaru arba’in da su ba da fifiko wajen duba lafiyar jama’a, domin rigakafin ya fi magani.
Ya kuma bayyana cewa ciwon ido da yana ne kan gaba wajen kawo makanta a Najeriya, inda ya ce asibitin na gudanar da aikin tiyatar ido ga mutane kusan dubu 3 a duk shekara.
Sani Sulaiman/Wababe
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
