Kasuwanci
Gwamnan Kano Ya Kaddamar Da Rarraba Kayan Agaji Na Ramadan
Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano ya kaddamar da rabon kayan abinci na Ramadan karo na hudu ga mabukata da marasa galihu a kananan hukumomin jihar 44, tare da gargadi kan karkatar da kayan abinci.
Yusuf ya kaddamar da rabon ne a masana’antar shinkafa ta Tiamin da ke karamar hukumar Dawakin Kudu.
Da yake jawabi a lokacin bikin, gwamnan ya gargadi masu kula da rabon kayan agajin da su guji karkatar da su, yana mai jaddada cewa duk wanda aka samu yana karkatar da su za a hukunta shi kamar yadda doka ta tanada.
“Na rantse da Allah duk wanda aka samu yana karkatar da kayan agajin za a yi hukunci mai tsauri kuma bisa doka, wannan gwamnati ba za ta bari masu zagon kasa su sha ba,” inji shi.
Gwamnan ya ce dalilin wannan tallafin shi don saukaka wahalhalun da ake fuskanta, a lokacin azumin watan Ramadan.
Ya ce za a raba buhunan kayan masarufi 224,440 ga gundumomin Sanatoci uku da ke jihar domin ci gaba da rabawa wadanda za su ci gajiyar shirin.
Ya kuma nemi afuwar al’ummar jihar kan hakurin da suka nuna a lokacin da ake sarrafa shinkafar da buhu domin rabawa.
Gwamna Yusuf ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da shiga tsakani “har sai an kawar da yunwa a tsakanin mutanenmu.”
Ya godewa gidauniyar Aliko Dangote da sauran kungiyoyi da daidaikun jama’a da suka raba nasu kayan agajin ga mabukata a cikin wannan wata mai alfarma, ya kuma yi addu’ar Allah ya saka musu da alheri.
Tun da farko, Shugaban Kwamitin Rarraba tallafin, Dakta Abdullahi Baffa Bichi, ya ce wannan rabon shi ne na hudu a cikin shirin rabon kayan abinci ga jama’a.
Bichi, wanda kuma shi ne sakataren gwamnatin jihar, ya yabawa gwamna Yusuf bisa wannan karimcin, wanda yace zai rage musu wahalhalu.
ABDULLAHI JALALUDDEEN KANO/Wababe
-
Labarai6 days ago
Wajibi Ne a kammala Aikin Hanyar Abuja Zuwa Kano Nan da Watanni 14 – FG
-
Labarai5 days ago
Hukumar Shige da Fice Ta Gargadi Jama’a Kan Sabuwar Kungiya Achad Life Mission
-
Labarai2 days ago
Hukumar Alhazai Ta Jihar Jigawa Ta Samar Da Masauki Na Alfarma Ga Alhazan Jihar
-
Kasuwanci6 days ago
Na Biya Dala Dubu 3 Don a Asirce Mijina Ya Mayar da Auren Mu – Bose
-
Labarai4 days ago
Gwamnatin Neja Ta Haramtawa Motocin Da Suka Fito Daga Hanyar Maje Bin Gadar Dikko
-
Labarai6 days ago
Gwamnatin Jihar Kano Ta Dawo Da Ayyukan Ma’aikatar Yada Labarai
-
Labarai5 days ago
Majalisar Dattijai Ta Bukaci Karfafa Jarin Bankin Lamunin Gidaje Na Tarayya
-
Labarai6 days ago
Gwamnatin Nijar ta soke biyan kudaden PTA a Makarantun Gwamnati