Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kaduna Ta Raba Tallafi Ga Wadanda ‘Yan Fashin Daji Suka Raba Da Gidajen su

Published

on

Gwamnatin jihar Kaduna ta fara rabon kayan abinci ga ‘yan gudun hijira sama da dubu daya da ‘yan fashi daji suka raba da gidajensu a karamar hukumar Kajuru.

 

Mataimakiyar gwamnan jihar, Dakta Hadiza Balarabe da ta kaddamar da rabon kayayyakin a karamar hukumar Kajuru ta ce gwamnati ta kudiri aniyar samar da yanayi mai aminci da wadata ga kowa da kowa kuma ba za ta huta ba har sai an kawar da barazanar ‘yan fashin daji.

 

Dokta Balarabe wanda mataimakin shugaban ma’aikata a ofishinta, Mista James Kanyip ya wakilta, ya bayyana cewa, a matsayinsu na gwamnati, ya zama wajibi su tabbatar da tabbatar da walwala da jin dadin al’ummarta, musamman a wannan lokaci da suke cikin mawuyacin hali.

 

Ta ce Gwamna Uba Sani ya fahimci radadin da suke ciki sakamakon rashin tausayi da Imani da aka nuna musu don haka ba a za ayi kasa a gwiwa ba wajen basu taimako da tallafi ga wadanda abin ya shafa.

 

A cewar Dokta Balarabe, kayayyakin tallafin da aka raba sun hada da manyan motoci guda biyu da garin masara da kuma shinkafa.

 

Da yake jawabi ga ‘yan gudun hijirar, Sakataren zartarwa na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna KADSEMA, Dokta Usman Mazadun ya ce kimanin ‘yan gudun hijira dubu dari biyu da casa’in ne aka samu a kananan hukumomi 12 na jihar Kaduna.

 

Mista Mazadun ya bayyana cewa a karamar hukumar Chikun, matsalar rashin tsaro ta shafi al’ummomi 134 da kuma mutane 26,345 da suka rasa matsugunansu yayin da a Birnin Gwari, al’ummomi 84 da abin ya shafa kuma 70,893 suka rasa matsugunansu.

 

Dakta Usman Mazadun ya kuma bayyana cewa nan da ‘yan makonni masu zuwa gwamnati za ta mika rabon tallafin ga daukacin al’ummomin da abin ya shafa a kananan hukumomi 12 da aka tantance.

 

Da yake magana da manema labarai, shugaban karamar hukumar Kajuru, Mista Ibrahim Gajere, ya bayyana fatansa cewa, ‘yan gudun hijira na karamar hukumar Kajuru ne suka fara cin gajiyar tallafin.

 

A nasa jawabin, Basaraken Kufana Gwan Kufana, Mista Titus Dauda, ​​ya nuna matukar godiya ga Gwamnan, da kuma tawagarsa bisa namijin kokarin da suke yi na ganin an kai agaji ga wadanda suka fi bukata.

 

Ya bayyana cewa aikin alheri ba wai kawai samar da ababen more rayuwa ba ne, har ma ya kara dankon zumunci tsakanin gwamnati da jama’a.

 

 

Wadanda suka ci gajiyar tallafin, sun nuna jin dadinsu ga jihar Kaduna bisa samar da tallafin da suka hada da Shinkafa da garin tuwa.

 

Aminu Dalhatu/Wababe

Labarai

Labarai13 hours ago

Gwamnatin Jigawa Za Ta Samar Da Tarakta 300 Ga Manoma Daga Amurka

A kokarinta na ci gaba da habbaka harkokin noma, Gwamnatin Jihar Jigawa ta ƙulla wata yarjejeniyar haɗin gwiwa da wasu...

Labarai13 hours ago

An kama masu zanga-zanga 17 a jami’ar Texas

An sake kama ƙarin mutanen da ke da alaƙa da zanga-zangar nuna goyon baya ga Falasɗinawa inda a wannan karon...

Labarai1 day ago

An Samar Da Masauki Kusa Da Harami Ga Alhazan Jihar Jigawa

Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Jigawa  ta samar da katafaren masauki  kusa da Masallacin Harami da ke birnin Makkah...

Labarai3 days ago

Kungiyar AFAN Ta Shirya Taron Bita Ga Manoman Jihar Jigawa

Hadaddiyar kungiyar manoma ta kasa reshen Jihar Jigawa da cibiyar binciken yanayin kasa dake Kaduna sun shirya wa manoma daga...

Fasaha4 days ago

An Bukaci Gwamnatin Sakkwato Ta Agaji Jami’ar Jihar

Kungiyar Malaman Jami’ar Jihar Sakkwato ASUU-SSU ta yi kira ga gwamnatin Jihar ta duba halin da kungiyar ke ciki da...

Kasuwanci4 days ago

Mun Aika Musu Takardun Gargadi Kafin Ginin Ya Rushe – KANUPDA

  Manajan Daraktan Hukumar Tsare-tsare da Ci gaban Birane ta Jihar Kano (KNUPDA), Architect Ibrahim Yakub Adamu ya yi gargadin...

Ilimi4 days ago

Zamu Zuba Jarin Dala Miliyan 600 a Nijeriya – Mr. Robert

Shugaba Kasa Bola Tinubu ya samu masu zuba jarin dala miliyan 600 daga kamfanin sufurin jiragen ruwa na kasar Denmark,...

Labarai6 days ago

Gini Ya Fado Kan Mutane 11 A Kano

Wani gini ya fado kan ma’aikata suna tsaka da aikin gini a unguwar Kuntau da ke Karamar Hukumar Gwale a...

Ilimi6 days ago

Gwamnatin Qatar Za Ta Tallafa Wa Marayu 1000 A Borno

Gwamnatin Kasar Qatar ta yi alkawarin tallafawa kimanin marayu dubu daya da rikicin Boko Haram ya rutsa da iyayensu. Jakadan...

Labarai1 week ago

Jihar Jigawa Za Ta Fara Allurar Rigakafi Da Bada Unifom Ga Alhazai

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce nan ba da dadewa ba za ta fara gudanar da allurar...

Mafi Shahara