Labarai
Guguwa ta kashe mutum daya, ta kuma lalata gidaje sama da 100 a Nasarawa

Wata kakkarfar Guguwar ta kashe mutum daya tare da jikkata wasu da dama tare da lalata gidaje sama da dari a Agbashi da ke karamar hukumar Doma a jihar Nasarawa.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, mataimakin shugaban karamar hukumar Doma Mista John Bako – Ari, ya ce abin takaicin ya faru ne a ranar Talata da yamma.
A cewarsa, sama da gidaje dari ne aka lalata da suka hada da babban masallacin Agbashi, wani bangare na makarantar furamare ta Agbashi da sauran kayayyakin more rayuwa da dama na jama’a.
“A gaskiya guguwar ta lalata gidaje sama da 100 da suka hada da, masallaci da kuma makarantar Firamare, lamarin ya faru ne jiya da yamma,” inji shi.
Shima da yake magana akan lamarin, mukaddashin shugaban kungiyar ci gaban Agbashi, Mista Anthony Oshinyeka, mukaddashin shugaban kungiyar ci gaban yankin, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici.
Ya kuma yi kira ga gwamnati da ta gaggauta kawo dauki domin dakile mummunar barnar da al’ummar Agbashi ke fama da shi.
Mukaddashin Shugaban kungiyar ya nemi da a gaggauta bada kayan agaji daga gwamnati da masu hannu da shuni ga al’ummomin da abin ya shafa.
Aliyu Muraki/Lafia/Wababe
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai23 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
