Labarai
Gwamna Kefas ya ziyarci Takum Inda guguwa ta lalata gidaje sama da 100 a Taraba

Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba ya tabbatar wa mazauna garin Takum cewa gwamnati za ta nemo hanyoyin tallafawa don sake gina gidajen da guguwa ta lalata a yammacin ranar Talata.
Wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai ya raba wa manema labarai, ta ce Kefas ya bayar da wannan tabbacin ne a ranar Laraba a ziyarar da ya kai yankin.
Idan ba a manta ba a ranar Talatar da ta gabata ce ruwan sama kamar da bakin kwarya ya lalata gidaje da dama, lamarin da ya sa mazauna yankin da dama suka rasa matsuguni.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, Dr. Kefas ya fara tura tawagar jami’an jihar zuwa Takum domin tantance barnar da aka yi.
Daga bisani kuma Gwamna Kefas ya ziyarci Takum domin gani da idon sairin barnar da iskan ya yi.
Yayin zagaya wasu yankunan da abin ya shafa na birnin, gwamnan ya jajanta wa wadanda abin ya shafa tare da gabatar da kalaman karfafa gwiwa.
Bugu da kari, gwamnan ya gana da shugabannin al’umma da mazauna yankin, ya ba su tabbacin gwamnati a shirye suke na tallafawa wajen sake gina gidajensu da suka lalace.
Mazauna garin Takum da suka fito kan tituna domin tarbar gwamnan, sun bayyana jin dadinsu da daukar matakin da ya dace cikin gaggawa.
Sani Sulaiman/Wababe
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai22 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
