Labarai
Gwamnatin Tarayya za ta kara yawan mutanen da za ta bai wa tallafin kudi

Gwamnatin Tarayya na shirin sake fara bai wa talakawan kasar da kuma mafiya rauni miliyan 12 kuɗaɗen tallafi.
A halin yanzu, kusan mutane miliyan uku ne ke amfana da wadannan shirye-shiryen na tallafi, amma saboda tsadar rayuwa, gwamnati na sa ran karin iyalai miliyan 12 za su cancanci karɓan wadannan kudade.
Ministan kudi da tattalin arziki, Wale Edun, ne ya sanar da wannan shirin yayin wani taron ma’aikata a Uyo, da ke jihar Akwa-Ibom.
Ministan ya ce manufar ita ce a bayar da tallafin kuɗi ga al’ummar da ke fuskantar ƙalubalen tattalin arziki da domin magance buƙatunsu na gaggawa, ta yadda za a rage talauci.
Shawarar sanar da shugaba Tinubu kan shawarar kwamitin ɗin kafin a kammala rahoton karshe shi ne a sanar da shi abubuwan da ke faruwa.
Edun ya jaddada yin amfani da fasaha don tabbatar da biyan kuɗi mai inganci da gaskiya, da guje wa ayyukan hannu da jinkiri.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
