Labarai
An Gina Riyojin Burtsatse ga yankunan da aka kai hari a Jihar Plateau

Asusun tallafaws wadanda wata masifa ta fadawa ya gina riyojin burtsatse ga wasu al’ummomi da rikicin baya bayan nan ya Shafa a jihar Plateau.
Mai bada shawara na musamman ga shugaban asusun Janar Theophilus Danjuma, Mrs Toyosi Akenrele-Ogunsiji tace asusun na da manufar yaye wahalhalun da ‘yan Nijeriya suke sha.
Wakilinmu Josiah Buzun na dauke da karin bayani daga Jos.
Hare haren da aka rika kaiwa wasu kananan hukumomin jihar Plateau yayi sanadiyar jama’a da dama suka rasa kayyakin more rayuwarsu.
Wannan ne dalilin da ya sa asusun tallafawa wadanda masifa ta Shafa karlashin jagorancin Janar Theophilus Danjuma ya tona riyojin burtsatse don samarda ruwan sha ga al’umma.
An gina wadannan riyojin masu aiki da hasken Rana ga al’ummomin Doruwa, Babuje da Gassa a karamar hukumar Barikin Ladi, Sai Kuma a Ariri dake karamar hukumar Bassa da Kuma al’ummomin Sop dake tsalleken dogo a karamar hukunar Riyom.
Mrs. Akenrele Ogunsiji da ta wakilci shugabar asusun wajen bude wadannan ayukkan, tace mutane na bukatar tsaftaccen ruwan sha da wasu kayyayakin more rayuwa, don haka suke fara raba hatsi da Kuma kayan koyarwa da Kuma tallafawa don karfafa jama’a su dogara da kansu.
Mrs. Akenrele Ogunsiji tayi bayanin cewa, duk Wanda ke musu aiki da ya kasa gabatar da shi yanda ya dace zasu hukunta shi.
Shi kuma babbar daraktan asusun Farfesa Nana Tanko tace wajibi kowa ya amfana da wadannan riyojin da aka tona.
A jawabinsa babban sakataren hukumar bada agajin gaggauwa na jihar Plateau Mr. Sunday Abubu ya hori wadanda suka amfana da wannan aikin su kula da shi sosai.
Shugaban al’ummar Gassa da ke karamar hukunar Barikin Ladi James Toma ya godewa wannan asusun da shugabansa Janar Theophilus Danjuma saboda sanya farin cikin a tsakanin talakawan kasan Nan.
Wadanda suka amfana da shirin bayan yabon wannan asusun sun kuma bayyana imanin cewa wannan aikin zai taimaka wajen samar da ruwansha mai tsafta tare da kawarda cutuka da ake samu daga ruwa tare da fatan za a Sami Karin irin wannan aikin.
Josiah/Shafii Wababe
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
