Labarai
Gwamnatin Tarayya Ta Bada Buhunan Abinci 36,000 Ga Jihar Borno
Gwamnatin tarayya ta baiwa gwamnatin jihar Borno tallafin buhunan abinci dubu talatin da shida da dari biyu da goma sha hudu masu nauyin kilogiram hamsin.
Da take gabatar da kayayyakin ga Gwamnan Jihar Farfesa Babagana Zulum, Darakta Janar ta Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta kasa NEMA, Hajiya Zubaida Umar ta ce kayayyakin na daga cikin tan dubu arba’in da biyu na hatsi da aka fitar daga runbun gwamnati.
Shugabar hukumar wacce darakta janar na shiyyar Arewa maso Gabas, Malam Yakubu Sulieman, ya wakilce ta, ta bayyana cewa bada tallafin kayan abinci na daga cikin shirin rage tasirin tabarbarewar tattalin arzikin da ake fama da shi a yankin.
“Shugaban kasa ya amince da fitar da kayayyakin abinci har ton 42,000 daga runbun gwamnatin tarayya da ke karkashin kulawar ma’aikatar noma da samar da abinci ta, a don haka mun zo ne domin mika kayayyakin ga gwamnatin jihar Borno inda za ta raba ga wadanda suka cancanta”.
A jawabinsa, Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya jinjinawa gwamnatin tarayya bisa wannan karamci ga al’ummar jihar, musamman wadanda rikicin Boko Haram ya shafa.
Ya kuma baiwa shugaban kasa da hukumar bada agajin gaggawa ta kasa tabbacin cewa za a raba kayan abincin da aka bayar ga marasa galihu a jihar.
“Ina kuma tabbatar muku da cewa ba za a samu karkatar da kayayyakin a jihar Borno ba, za a raba bisa cancanta ga al’ummar jihar.” Inji Zulum.
Gwamna Zulum ya kuma yabawa gwamnatin tarayya bisa bada gudunmawa a yunkurin da gwamnatin sa ke yi na sake tsugunar da wadanda rikici ya daidaita.
Shi ma a nasa jawabin, Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar SEMA, Dokta Muhammed Barkindo ya ce za a ba da fifiko ga gidaje suka rasa mahaifinsu da marasa lafiya da kuma masu fama da lalurar nakasa.
Kayayyakin da aka bayar sun hada da buhunan Masara 11,880, buhunan dawa 19,440 da buhunan Gero 5,130.
Dauda Iliya
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
