Ilimi
Gwamnatin Jihar Kaduna Za Ta Gina Sabbin Makarantun Sakandare 50 A Fadin Jihar
Gwamnatin Jihar Kaduna ta kammala shirye-shiryen bayar da aikin gina makarantun sakandare 50 a fadin jihar.

Gwamnan jihar Malam Uba Sani ne ya sanar da hakan a lokacin da yake kaddamar da sabuwar babbar sakandare da aka gina a Rigachikun da ke karamar hukumar Igabi ta jihar.
Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa, makarantar ta Rigachikun na daya daga cikin makarantun sakandire guda 62 da aka bada aikin gina su da kuma gyara a rukunin farko na shirin farfado da ilimi da gwamnatinsa ta sanya a gaba.

A cewarsa, an kammala akasarin ayyukan da aka bada tare da kaddamar da su, yayin da ake gab da kammala sauran.
Uba Sani ya yi nuni da cewa, ko shakka babu sabuwar makarantar sakandaren za ta samar wa dalibai yanayin karatu mai kyau.
“Idan za ku iya tunawa lokacin da na kaddamar da harsashin ginin wannan makaranta a ranar 31 ga watan Agustan 2023, na yi alkawarin cewa za a yi gaggawar kammala ta, yau gashi cikin ikon Allah an cimma gacci”. Inji shi.

A cewarsa, hakan na nuni da gagarumin mataki a kokarin gwamnatinsa na magance daya daga cikin manyan matsalolin da ke kawo cikas ga fannin ilimi.
Hakazalika, Gwamnan ya kuma kai ziyarar gani da ido cibiyar koyar da sana’o’i da ake ginawa a Rigachikun.
Aminu Dalhatu
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
