Labarai
Gwamnatin Jihar Kano Za Ta Yi Gwajin Tarin Fuka Kyauta Ga Kananan Yara
Gwamnatin jihar Kano za ta yi wa yara 6,000 a cibiyoyin lafiya 1,346 gwajin cutar tarin fuka kyauta.
Kwamishinan lafiya na jihar Dr. Abubakar Labaran Yusuf ne ya bayyana hakan a lokacin da yake ganawa da manema labarai domin tunawa da makon gwajin cutar tarin fuka na kasa na shekarar 2024.
A cewarsa bikin ya kasance na musamman, domin an hada shi da sauran ayyukan kiwon lafiya kamar su abinci mai gina jiki, cuta mai karya garkuwar jiki ta HIV, wayar da kan al’umma, da sauransu.
Kwamishinan ya bayyana cutar tarin fuka a matsayin cuta mai saurin yaduwa, wacce ke bin iska kuma gaba daya tana shafar huhu da ma wasu gabobin jiki.
Dr. Abubakar ya yi nuni da cewa, ana iya kamuwa da ita daga mai dauke da nau’in cutar zuwa wani wanda akasari ta hanyar tari, atishawa, magana ko dariya, wanda alamomin ta suka hada da tari na tsawon makonni biyu ko fiye da zazzabi mai alaka da shi ko kuma ba tare da shi ba, rage nauyi ko zufa cikin dare.
“Wasu alamomin da ke da alaƙa a jikin yara na iya haɗawa da rashun kuzari, fitar jini yayin tari, da kumburin wasu gabobi da rashin cin abinci“. Inji shi.
Ya ci gaba da cewa yaran da ke dauke da cutar tarin fuka ko kuma wadanda ba a kula da su ba za su iya yada ta zuwa kusan mutane 10 zuwa 15 a cikin shekara guda, inda ya bukaci iyaye da su kai ’ya’yansu don yin gwajin cutar kyauta.
“Hakkin ‘ya’yanmu ne a yi musu gwajin cutar tarin fuka, ya zama wajibi a matsayinmu na iyaye mu tabbatar da lafiya da walwalar ‘ya’yanmu kuma ya zama wajibi ga gwamnatin jihar Kano ta samar da ababen da za su dakile yaduwar cutar”.
Dokta Abubakar ya ci gaba da cewa, gwamnatin jihar Kano tare da hadin gwiwar ma’aikatar lafiya ta tarayya ta shirya shirin yaki da cutar tarin fuka da kuturta, inda aka samar da kayan aiki da magunguna da kwararrun ma’aikata da sauran kayayyakin da ake bukata.
Ciki har da injinan yin hoton jiki na X-Ray guda 20 da na gwajin kwayoyin cututtuka wato microscopes guda 250, da na’urorin gwajin cutar HIV da ta tarin fuka, da sauransu.
Kwamishinan ya bukaci ‘yan jarida da su kara himma wajen wayar da kan jama’a game da illar cutar tarin fuka da kuma muhimmancin kai ‘ya’yansu domin yi musu gwaji da kuma yi musu magani.
Khadijah Aliyu
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
-
Labarai2 days ago2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro
