Connect with us

Labarai

Gwamnatin Jigawa Ta Kaddamar Da Harsashin Ginin Dindindin Na Kwalejin Jinya Ta Hadejia

Published

on

Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya kaddamar da bikin aza harsashin gina rukunin dindindin na kwalejin  jinya da ungozoma da ke Hadejia na naira biliyan biyar da rabi domin samar da isassun ma’aikata da kwararru a fannin lafiya.

Gwamnan ya bayyana cewa ingantaccen tsarin kiwon lafiya wani muhimmin alkawari ne da aka yi gabanin zabe wanda aka sanya shi cikin tsare-tsare guda 12 don ci gaban jihar Jigawa baki daya.

Ya ce aikin wanda ya kasu kashi biyu, ana sa ran kammala shi a cikin watanni 18 inda za a kashe naira biliyan 3 da kuma Naira biliyan 2 da rabi bi da bi.

Mallam Umar Namadi ya ci gaba da cewa, gwamnatin sa ta kuma yi niyyar samar da babban asibiti  a kowace mazabar majalisar jiha 30 da kuma cibiyar kula da lafiya a matakin farko a kowace gunduma.

Ya ce, wannan kari ne ga asibitocin kwararru da aka kafa a  shiyyoyi  t3 na jihar.

Namadi ya kuma ce, domin tabbatar da isassun ma’aikatan lafiya, gwamnati ta tura sama da dalibai 109 zuwa kasar Cyprus don yin karatun likitanci, tare da karin karatu a cikin gida.

Ya yi nuni da cewa, akwai kwalejojin aikin jinya da ungozoma guda uku a Birninkudu, Babura, da Hadejia, Gwamnan ya ce yana da kwarin guiwar samun ma’aikatan lafiya kwararru.

 

Usman Muhammad Zaria

Labarai

Labarai20 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai22 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara