Connect with us

Labarai

Jirgin Farko Na Alhazan Jihar Kano Ya Isa Kasa Mai Tsarki

Published

on


Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya kaddamar da jirgin farko na maniyyata aikin hajjin bana a jihar.

 

Da yake jawabi yayin kaddamarwar, Gwamna Abba Kabir  ya bukaci maniyyatan da su kasance jakadu nagari tare da yin addu’a ga jihar da  Najeriya  baki daya.

Jirgin na farko na mahajjatan  Kano ya tashi ne daidai da karfe goma sha daya da minti arba’in da daya na safiyar yau dauke da  jimillar mutane 578, a jirgin sama na Max Air B747  inda suka nufi filin jirgin sama na Sarki Abdul-Aziz da ke Jiddah.

Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa ya ce mahajjatan da ke  jirgin farkon sun fito ne daga kananan hukumomi hudu na jihar.

A cewarsa, karamar hukumar Gwale na da mahajjata 175, yayin da karamar hukumar Dala ke da alhazai 119, sai  karamar hukumar Ungogo tana da alhazai 106, ita kuma karamar hukumar Fagge na da mahajjata 135.

Ya kuma nuna jin jinjinawa Gwamna bisa karamcin da ya yi wa Alhazai da suka hada da tallafin kudin Hajji na Naira 500,000 kowanne, da karin kudin guzuri da ya kai sama da Naira miliyan 367, da karin Riyal 100  da aka bai wa dukkan maniyyatan.

 

Abdullahi Jalaluddeen

Labarai

Labarai20 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai22 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara