Labarai
Rukunin Farko Na Alhazan Jihar Borno Ya Isa Madina
Rukunin farko na maniyyata 383 daga jihar Borno ya isa garin kasa mai tsarki da safiyar yau Litinin tare da ragowar maniyyata 27 daga jihar Yobe.
Jihar Borno na da jimillar maniyyata 1,815 da ake sa ran za a yi jigilar su zuwa aikin Hajjin bana.
Da yake jawabi ga rukunin na farko na maniyyatan a filin jiragin sama na Muhammadu Buhari da ke Maiduguri, mataimakin gwamnan jihar Borno, Alhaji Umar Kadafur ya bukace su da su bi dokokin kasar Saudiyya sau da kafa.
Ya kuma bukace su da su yi addu’ar samun dauwamamman zaman lafiya a jihar da kasa baki daya.
A wata hira da gidan rediyon Najeriya a Maiduguri, mukaddashin shugaban hukumar jin dadin alhazai ta jihar Borno, Alhaji Dawule Mainok ya ce rukunin na farko ya kunshi maza 234 da mata 149.
Ya yi kira ga maniyyatan da su kasance jakadu nagari yayin da suke kasa mai tsarki.
Biyu daga cikin mahajjatan Aisha Ali daga Ngala da Idris Allamin daga karamar hukumar Konduga sun bayyana aikin tantancewar a matsayin maras cikas, sun yabawa hukumar alhazai ta kasa da hukumar alhazai ta jiha bisa jajircewa wajen ganin komi ya tafi yadda ake bukata.
Dauda Iliya
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
