Kasuwanci
An Horar Da Manoma 41 Kan Noman Kayan Lambu A Kano
Wata Kungiya mai zaman kanta (NGO) ta da ake kira Netherland African Business Council (NABC) a turance, ta ce ta horar da manoma 41 kan noman kayan lambu don bunkasa wadatar abinci a jihar Kano.
Babban Jami’ar ayyukan kungiyar Hajiya Fauziyya Sadiq ta bayyana haka a wajen rufe taron horar da manoma na tsawon mako 16 a Kano.
Ta bayyana cewa horon na da nufin bunkasa aikin gona da masu zaman kansu a fannin noma a Najeriya.
A cewarta, jigon shirin na masu horas da manoman shi ne don inganta kwarewar kwararru, wadanda suka hada da wakilan kamfanonin da dillalan kayan lambu.
“An horar da manoman ta hanyar yanar gizo da kuma a fili akan ayyukan noma da taki da ban ruwa da kare amfanin gona da sauransu,” in ji ta.
Da take jawabi a madadin wadanda suka ci gajiyar tallafin, Fatima Muhammad ta yabawa hukumar ta NBC bisa wannan karimcin.
“Hakika wannan babban ci gaba ne. Mun sami sabon ilimi kan noman kayan lambu don haɓaka samar da kayan lambu,”
Ta yi alkawarin ba da ilmin da aka samu daga horon zuwa ga al’ummarsu.
Gidan Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, kungiyar ‘yan kasuwan Afrika ta Netherland (NABC) ce ta shirya wannan horon karkashin jagorancin Wageningen Plant Research.
KHADIJAH ALIYU/Wababe
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
