Labarai
Shirin Noma Abinci a Renewed Hope
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bayyana muhimman nasarori da ta cimma a fannin noma da tabbacin isasshen abinci, karkashin shirin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Renewed Hope.
Rahoton rabin wa’adi na aiki daga watan Mayu 2023 zuwa Afrilu 2025, wanda Ofishin Mai Baiwa Shugaban Kasa Shawara kan Tsare-Tsare da Hadin Gwiwa ya fitar, ya bayyana ayyukan da Ma’aikatar Noma da Tsaron Abinci ta gudanar domin cika alkawurran yakin neman zaben shugaban kasa.
Daya daga cikin manyan nasarorin da aka samu a rahoton shi ne sabunta da inganta dakunan ajiya na abinci na kasa, wanda ya taimaka wajen rage karancin abinci da daidaita farashi a kasuwanni.
Ma’aikatar ta kuma kaddamar da ayyukan gina hanyoyin ban ruwa da tafkunan ruwa domin kara yawan amfanin gona a duk shekara. Bugu da kari, an gudanar da shirin share filaye masu fadi domin kara yawan filayen noma.
A wani bangare, gwamnati ta aiwatar da shirye-shiryen musamman domin tallafawa matasa da mata masu sha’awar harkar noma. An hada da horaswa, tallafin kudi, da samar da hanyoyin samun abinci da kudin shiga ga iyalai, domin rage fatara da bunkasa yankunan karkara.
Haka kuma, an mayar da hankali wajen tabbatar da cewa kayan gona na fitar kasashen waje sun cika ka’idojin lafiya da inganci na duniya. Wannan ya baiwa Najeriya damar kara samun kudin shiga daga fitar da amfanin gona.
Ma’aikatar ta kuma karfafa aiwatar da muhimman sassa na shirin National Livestock Transformation Plan (NLTP) da ke karkashinta, wanda ya hada da samar da wuraren kiwo, shuka ciyayi da kula da dabbobi. Wannan ya taimaka wajen rage rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya da kuma kara yawan kiwo.
Rahoton ya nuna cewa nasarorin da aka samu sun yi daidai da alkawurran da Shugaba Tinubu ya dauka a lokacin yakin neman zabe, inda ya yi alkawarin tabbatar da wadatar abinci da bunkasar tattalin arzikin kasa ta hanyar noma.
Jami’an gwamnati sun jaddada cewa za su ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen da za su karfafa bangaren noma, su samar da ayyukan yi, da kuma bunkasa rayuwar al’umma.
Bello Wakili
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
