Ilimi
PCN Ta Kai Ziyara Ga Hukumar Samarda Magunguna Ta Jihar Kano
Hukumar Kula da Magunguna ta Najeriya (PCN) ofishin Kano ta kai ziyarar gani da ido ga hukumar samar da magunguna ta jihar Kano (DMCSA).
Wannan ziyarar alama ce ta farkon tsarin ba da izini ga DMCSA don zama cibiyar rarraba magunguna ta mega da cibiyar bada horo.
Jami’ar Jihar Kano mai kula da ofishin PCN Kano Pharmacist Hasiya Abubakar Ladan ce ta jagoranci tawagar da suka kai ziyarar.
Wannan ziyarar wani mafari ne na tantancewa da wata tawagar kwararru daga hedikwatar PCN ta kasa da ke Abuja.
Ta bayyana cewa ziyarar na da nufin tantance yadda DMCSA ke bin ka’idoji, don ba da Takaddar Rijistar wuraren sayarda magunguna.
Pharmacist Ladan ta yabawa shugabannin DMCSA bisa yadda suke tafiyar da ayyukan kungiyar yadda ya kamata tare da nuna gamsuwa da matakin da hukumar ta dauka.
Darakta Janar na DMCSA Pharmacist Gali Sule, ya tarbi tawagar inda ya zagaya da su a rumbunan adana kayayyaki.
Ya bayyana cewa hukumar ta dakatar da samar da magunguna domin inganta sashin sarrafa magunguna kamar yadda PCN da NAFDAC suka bada shawara.
Pharmacist Sule ta godewa tawagar bisa ziyarar da suka kai tare da ba su tabbacin hadin kan DMCSA a duk lokacin da ake gudanar da aikin tantancewa.
KHADIJAH ALIYU/Wababe
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
