Ilimi
Gwamnatin Niger Ta Karbi Yara 21 Da Aka Ceto
Gwamnatin jihar Neja ta karbi yara ashirin da daya da aka kama a kan iyakar Najeriya da jamhuriyar Nijar yayin da ake safarar su zuwa Sudan.
Mataimakin gwamnan jihar, Kwamared Yakubu Garba wanda ya bayyana haka a lokacin da yake karbar yaran a madadin gwamnatin jihar Neja a Minna, ya ce an kama yaran ne a cikin kasashen Kamaru da Mali da Jamhuriyar Nijar da kuma Sudan.
Kwamared Yakubu Garba ya bayyana cewa yaran da aka ceto ‘yan karamar hukumar Magama ne a jihar Neja, amma ya yaba da kokarin gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro da kuma hukumar fataucin bil’adama bisa nasarar ceto yaran.
Ya ci gaba da cewa ta’addancin ya saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya sashe na 34 karamin sashe na 1 da sashe na 13 na kundin tsarin mulkin kasa da ya haramta duk wani nau’in safarar mutane a kasar.
Da yake mayar da martani, daya daga cikin iyayen yaran da aka ceto, Jamilu Usman wanda ya bayyana ‘ya’yansa biyu Umar Jamilu mai shekaru 6 da Maruf Jamilu mai shekaru 5 ya bayyana cewa Malam Abubakar sananne ne a wurinsu wanda ya yi karatu a Jamhuriyar Nijar.
Ya bayyana cewa sun ba wa ‘ya’yansu damar tafiya da Malam Abubakar Jamhuriyar Nijar domin samun ilimin addinin Musulunci, inda ya jaddada cewa shi ne shugaban makarantar firamare ta Tungan Gari da ke karamar hukumar Magama, yana da mata hudu da ‘ya’ya talatin kuma zai ajiye aiki nan da shekaru biyar masu zuwa, shi ne ya sa suka bashi ‘ya’yansu.
Sai dai ya kara da cewa suna biyan dubu 35 ga kowane yaro kowane wata domin su sami damar samun ilimin da ake bukata.
KARSHEN ALIYU LAWA/Wababe
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
