Labarai
Uwargidan Gwamnan Jihar Kebbi Ta Yi Kiran A Yiwa Mijinta Addu’a

Uwargidan Gwamnan Jihar Kebbi, Hajiya Zainab Nasir Idris, ta ce addu’a ita ce ginshikin duk wani shugabanci mai nasara, don haka ta yi kira ga jama’a da kungiyoyi da su yi wa gwamnatin mijinta addu’ar samun nasara.
Uwargidan Gwamnan, ta bayyana haka ne a lokacin da ta kai ziyarar ban girma
‘ya’yan kungiyar matan ma’aikatan jami’an hukumar kula da shige da fice ta Kasa (IMOWA) Jihar Kebbi BABI.
Yayin da take bayyana jin dadin ziyarar, Hajiya Zainab Idris ta ce kofofinta a bude suke domin tattaunawa mai ma’ana da daidaikun mutane da kungiyoyi domin ci gaban jihar.
Tun da farko shugabar kungiyar matan jami’an shige-da-fice ta jihar Kebbi (IMOWA) Hajiya Aishatu Muhammad Sabo ta godewa uwargidan gwamnan bisa irin tarbar da aka yi musu, sannan ta yi addu’ar Allah ya shiryar da shugabannin jihar kan hanya madaidaiciya.
Hajiya A’isha Sabo, ta ce sun kai ziyarar ne domin godiya ga Gwamnan Jihar bisa goyon bayan da yake bai wa kungiyar da kuma da kuma kusanci kan ayyukan kungiyar, wadanda suka hada da tallafa wa ‘ya’yan Marigayi Jami’an kungiyar domin su ji a rai na rashin iyayensu.
Ta kuma gode wa Gwamnan Jihar bisa irin namijin kokarin da ya yi na gyara ofishin fasfo na jihar Kebbi na Hukumar Shige da Fice ta kasa, da karbar bakuncin Konturola Janar a Jihar, da samar da motocin aiki da kuma sanya Kwanturolan Jiha cikin Kwamitin Tsaro na Jihar sannan kuma ta yi kira ga Gwamnan Jihar. Uwargidan Gwamna don kula da ayyukan da take yi wa al’ummar jihar.
Abdullahi Tukur/Wababe
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
