Connect with us

Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Raba Kayan Abinci Ga Dubban Iyalai A Jihar Kebbi

Published

on

Gwamnatin Tarayya ta fara rabon kayan abinci da na gina jiki ga dubban marasa galihu da kuma masu larurar nakasa a Jihar Kebbi.

Ministan Kasa a Ma’aikatar Harkokin Jin-ƙai da Rage Talauci, Alhaji Yusuf Tanko Sununu, wanda ya kaddamar da rabon a Birnin Kebbi, ya ce shirin ya nufin tallafa wa al’ummomin da suka fi rauni waɗanda bala’o’in jin-ƙai suka shafa a jihar.

Yusuf Sununu ya bayyana cewa shirin ya haɗa da rabon kayan gina jiki da magunguna ga asibitoci, cibiyoyin kula da yara, da sauran rukunonin da ke bukata. Ya ƙara da cewa za a kai irin wannan tallafi zuwa sauran mazabun sanatoci na jihar.

Ya ce shirin ya yi daidai da ajandar  sabuwar fata ta Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, wadda ke da nufin rage raɗaɗin da bala’o’in jin-ƙai ke haifarwa a ƙasar. Ya bayyana cewa kayan abincin sun haɗa da buhun shinkafa, gero, wake, masara, man girki, da sauran kayan gina jiki.

Da yake jawabi a wajen taron, Gwamnan Jihar Kebbi, Nasiru Idris, ya yabawa Gwamnatin Tarayya kan wannan tallafi, yana mai cewa shirin zai taimaka matuƙa wajen rage wahalhalun al’ummar jihar. Ya kuma tabbatar da jajircewar gwamnatinsa wajen haɗa kai da Gwamnatin Tarayya don rage talauci, yunwa da cututtuka.

Gwamnan ya yi kira ga waɗanda suka amfana da shirin da su yi amfani da tallafin yadda ya dace, tare da tabbatar musu da ƙarin tallafi nan gaba. Haka kuma ya buƙace su da su nuna godiya ta hanyar sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a wa’adi na biyu.

Rahoton Radio Nigeria ya nuna cewa wasu daga cikin waɗanda suka amfana sun yaba da ƙoƙarin gwamnatocin tarayya da jiha, inda suka tabbatar da cewa tallafin ya zo a kan lokaci kuma za su yi amfani da shi yadda ya kamata.

An kaddamar da shirin ne ta hannun gwamnan jihar tare da taimakon Ƙaramin Ministan Harkokin Jin-ƙai da Rage Talauci, a gaban manyan jami’an gwamnatocin tarayya da jiha.

COV: Sani Dutsinma

Gwamnatin Tarayya Ta Horar da Masu Shigo da Kaya da Masu Ruwa da Tsaki kan Kasuwanci

Gwamnatin Tarayya ta sake jaddada aniyarta ta ƙarfafa ƙa’idojin ɗa’a a harkar shigo da kaya a matsayin wani muhimmin mataki na ƙara kuɗaɗen shiga da bunƙasa tattalin arziƙin ƙasa.

Babban Sakataren Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayya, Mista Raymond Omenka, ne ya bayyana hakan a yayin wani taron wayar da kai na kwana guda ga masu shigo da kaya, hukumomin da ke da alhaki da sauran masu ruwa da tsaki. Taron ya gudana a Kano, mai taken “Ɗa’a a Harkar Shigo da Kaya don Inganta Tara Kuɗaɗen Shiga.”

Sakataren Dindindin ya bayyana cewa ɓangaren shigo da kaya muhimmin ginshiƙi ne a tattalin arziƙin ƙasa, inda ya ce yana taka rawar gani wajen samar da kayayyaki da ayyuka, ƙirƙirar guraben ayyukan yi, da sauƙaƙa hulɗar kasuwanci da ƙasashen waje.

Da take wakiltarsa, Mataimakiyar Darakta a Sashen Hulɗar Kasuwanci, Rukayyatu Abdullahi, ta ce damar da ke akwai na ƙara kuɗaɗen shiga ta hanyar bin ƙa’idojin ɗa’a a ɓangaren shigo da kaya babba ce ƙwarai. Ta jaddada cewa aiki da gaskiya da riƙon amana na samar da daidaito da adalci ga dukkan masu shigo da kaya.

A nasa jawabin babban bako, Daraktan Sashen Kasuwanci da Musayar Kuɗaɗe na Babban Bankin Nijeriya (CBN), Dakta Musa Nakoji, wanda Jamilu Ado ya wakilta, ya ce taron zai bai wa masu ruwa da tsaki damar amfani da ƙa’idojin ɗa’a a harkar shigo da kaya a fannoni daban-daban na kasuwanci da rayuwar ɗan Adam, wanda hakan zai ƙara ingancin tattalin arziƙi.

Daga cikin muhimman abubuwan da suka gudana a taron akwai gabatar da takardu daga Hukumar Kwastam ta Nijeriya, Hukumar Kula da Inganci ta Nijeriya (SON), Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC), da Ƙungiyar Masu Shigo da Kaya ta Nijeriya.

Fiye da mahalarta 151 ne suka halarci taron.

ABDULLAHI JALALUDDEEN, KANO

Labarai

Labarai20 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai22 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara