Connect with us

Labarai

Kashi 80 Na Masu Ajiya A Bankunan Da Aka Rufe Sun Karɓi Kuɗinsu – NDIC

Published

on

Hukumar Inshorar Ajiya ta Nijeriya (NDIC) ta bayyana cewa fiye da kashi 80 na masu ajiya a bankunan kasuwanci da aka rufe a Nijeriya sun karɓi kuɗaɗen inshorar da aka tanada musu.

Wani jami’i a Sashen Binciken Bankuna na NDIC, Zayyad Abubakar, ne ya bayyana hakan a yayin wani taron wayar da kai kan ayyuka da rawar da NDIC ke takawa. An shirya taron ne ga ɗaliban Makarantar ’Yan Mata ta Sakandare ta Gwamnati (GGSS) da ke Old Airport Road, Minna, Jihar Niger.

Zayyad Abubakar ya bayyana cewa dukkan kwastomomin da ke da cikakkun bayanai a tsarin banki, cikin kwanaki biyar bayan soke lasisin bankinsu, an biya su kuɗinsu kai tsaye ba tare da sun nemi hakan ta hanyar gabatar da ƙorafi ba. Sai dai ya ce waɗanda ba su da cikakkun bayanai a banki, kamar BVN da sauran muhimman sharuɗɗa, ba a iya biyan su ba.

Ya ƙara da cewa a bara NDIC ta karɓi kusan ƙorafe-ƙorafe 80, inda aka warware kimanin 50 daga ciki, aka kuma mayar wa waɗanda abin ya shafa kuɗinsu. Ya jaddada cewa ana miƙa duk wasu batutuwan satar kuɗi ga hukumomin tsaro, domin ba sa cikin ikon NDIC.

A cewarsa, fiye da kashi 80 na ɗaliban GGSS Minna suna da asusun banki sakamakon shirye-shiryen wayar da kan da NDIC ke yi kan juriyar kuɗi, samun kuɗin shiga don daidaito da ’yancin kai na kuɗi. Ya kuma ce sama da ɗalibai dubu biyu daga jihohi goma a dukkan yankunan ƙasar sun amfana da shirye-shiryen NDIC na wayar da kai kan shigar da jama’a harkar banki da ilimin kuɗi, wanda ke haifar da sakamako mai kyau.

A nasa jawbai kan Ranar Ajiya ta Duniya ta 2025, wani jami’i a Sashen Sadarwa da Hulɗa da Jama’a, Tanko Ibrahim, ya shawarci ɗaliban da su tsunduma cikin ƙananan sana’o’i domin dogaro da kai, tare da buɗe asusun banki don ajiya da zuba jari.

COV: Aliyu Lawal

Labarai

Labarai20 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai22 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara