Connect with us

Labarai

Gwamnatin Jigawa ta Amince da Shirin Ciyarwar Watan Ramadan na Bana

Published

on

Daga Usman Muhammad Zari

Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da gudanar da shirin ciyar da jama’a na buda-baki (Iftar) na shekarar 2026, da nufin tallafa wa marasa galihu, tare da tabbatar da cewa al’ummar jihar sun samu abinci mai gina jiki a lokacin watan Ramadan mai alfarma.

Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi, Dr Nura Ibrahim Kazaure, ne ya bayyana hakan jim kaɗan bayan taron majalisar zartarwa ta jihar da aka gudanar a Government House Dutse.

A cewarsa, shirin da aka amince da shi ya tanadi kafa cibiyoyin ciyarwa guda 640 a faɗin jihar.

Ya ce hakan ya haɗa da kafa cibiyoyi biyu a kowace daga cikin mazabun siyasa 287 da ke cikin ƙananan hukumomi 27 na jihar, da kuma cibiyoyi na musamman a manyan makarantu, gidajen gyaran hali, da cibiyoyin jin ƙai domin tabbatar da cewa kowa ya amfana da shirin.

Dr Kazaure ya nuna cewa ana sa ran shirin zai rika samar da abinci ga mutane sama da  264,600 a kowace rana,

A tsawon watan Ramadan, ana sa ran shirin zai samar da abinci sama da miliyan 23 da dubu 800 wanda za mutane sama da miliyan 7 da dubu 900 za su amfana.

Kazaure ya ce an tsara shirin ne domin samar da abinci mai gina jiki da inganci ga Musulmai masu azumi da sauran marasa galihu, tare da tallafa wa gidaje masu ƙaramin ƙarfi da kuma mutanen da ke fuskantar matsin tattalin arziki.

Ya ƙara da cewa shirin zai ƙarfafa zumunci a tsakanin al’umma, tausayi, da ɗaukar nauyin juna, tare da ƙara tallafa wa shirye-shiryen  zamantakewa da rage talauci da gwamnatin jihar ke aiwatarwa.

Sai dai Dr Kazaure ya bayyana cewa majalisar ta umarci a bi ƙa’idojin inganci sosai wajen sayo kayan abinci, girkawa da kuma rabawa.

Kwamishinan ya ƙara da cewa za a kafa kwamitocin sa ido a matakin jiha, ƙananan hukumomi da kuma unguwanni domin tabbatar da an aiwatar da shirin yadda ya kamata tare da rabon adalci.

Ya buƙaci shugabannin al’umma, cibiyoyin addini, ƙungiyoyin matasa da ƙungiyoyin fararen hula su bayar da cikakken haɗin kai domin tabbatar da nasarar shirin tare da kiyaye tsari a duk cibiyoyin ciyarwar.

Ya ƙara da cewa wannan shirin na jin ƙai da haɗa kan jama’a ya kuma shafi ma’aikatan gwamnati na jihar, waɗanda su ne ginshiƙin aiwatar da manufofin gwamnati a fannoni daban-daban.

 

 

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai1 week ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara