Labarai
Gwamna Lawal Ya Sami Lambar Yabo ta Gwamnan Shekara 2026
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya sake jaddada ƙudurin gwamnatinsa na samar da ci gaba mai ganuwa tare da dawo da amincewar jama’a ga harkokin mulki a jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake karɓar lambar yabo ta Gwamnan Shekara a taron shekara-shekara na karramawa da taron shugabanci da jaridar Leadership ta shirya, wanda aka gudanar a Abuja.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya bayyana cewa taron na shekara-shekara an tsara shi ne domin gano tare da karrama fitattun mutane da ayyukansu suka cancanci yabo da girmamawa a matakin ƙasa.
Sanarwar ta ƙara da cewa Mataimakiyar Babban Sakatariyar Majalisar Ɗinkin Duniya, Dakta Amina Mohammed, ce ta gabatar da jawabi a taron, wanda aka gudanar a ƙarƙashin taken: “Dorewar Siyasa da Ci gaba Mai Ɗorewa a Afirka a Cikin Tsarin Duniya Mai Cike da Ƙalubale: Taswirar Hanya ga Nijeriya.”
Sanarwar ta nuna cewa zaɓen Gwamna Lawal a matsayin Gwamnan Shekara na nuna gagarumin ci gaban da gwamnatinsa ta samu a muhimman fannoni daban-daban a Jihar Zamfara.
Ta ƙara da cewa jaridar ta ambaci bajintar gwamnan, jarumtakar jagoranci, da shirye-shiryen sauyi masu tasiri a matsayin wasu daga cikin dalilan da suka sa aka ba shi wannan lambar yabo.
Haka kuma, an bayyana ƙoƙarinsa a matsayin muhimmin ginshiƙi wajen sanya Zamfara a sabon tafarkin ci gaba, zaman lafiya, da bunƙasar da za ta ɗore.
Sanarwar ta kuma ce wannan karramawa za ta ƙara ƙarfafa gwiwar Gwamnatin Jihar Zamfara wajen ƙara himma a fannonin tsaro, sauya fasalin noma da raya karkara, faɗaɗa ababen more rayuwa, inganta ayyukan kiwon lafiya, haɓaka ilimi, da bunƙasa jarin ɗan Adam a faɗin jihar.
REL/AMINU DALHATU
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
