Connect with us

Labarai

Kwamitin Majalisar Dattawa Kan Kuɗi Ya Dakatar da Nazarin Kasafin Kuɗin 2026

Published

on

Kwamitin Majalisar Dattawa kan Kuɗi ya dakatar da ci gaba da nazarin kasafin kuɗin shekarar 2026 na Ofishin Babban Akanta na Tarayya.

A yayin zaman kare kasafin kuɗi da aka gudanar a wannan Alhamis, Kwamitin ya tsananta wa Babban Akanta na Tarayya, sakamakon matsalolin da ke hana ofishin gudanar da aikinsa yadda ya kamata.

A jawabin buɗe taro, Shugaban Kwamitin, Sanata Sani Musa, ya nuna bacin ransa tare da sukar Ofishin Babban Akanta kan ƙarancin sakin kuɗaɗe ga Ma’aikatun Gwamnati, Hukumomi da ke ƙarƙashin doka, da kuma abin da suka kira tsarin biyan kuɗi na bai da ke takura ’yan kwangila.

Ya nuna cewa halayyar ofishin ga kwamitin ba ta da kyau, kuma dole ne ta canza domin amfanin kowa da kowa.

Ya ce:“Ba za mu karɓi kasafinku ba har sai mun gamsu cewa ofishinku a shirye yake ya yi abubuwan da za su sa al’amura su inganta ga ’yan Nijeriya, tare da cikakkun tabbaci daga gare ku.”

Da suke bayyana ra’ayoyinsu a zaman, wasu sanatoci sun yi ƙorafi mai zafi kan dalilin da ya sa Ofishin Babban Akanta ya gaza sakin kuɗaɗe ga ’yan kwangila.

Sanata Muntari Dandutse ya bayyana mamakinsa kan yadda aka ruwaito cewa hukumomin tara kuɗaɗen shiga sun samar da naira tiriliyan 28, amma duk da haka kashi 85 na ’yan kwangila ana bin su bashin kuɗi, yayin da yawancin Ma’aikatun Gwamnati ba su samu ko sisin kwabo ba a ɓangaren kasafin kuɗin manyan ayyuka na shekarar 2025.

Haka kuma, Sanata Abdul Ningi ya nuna damuwarsa cewa yawancin ayyukan kwangila da aka tsara aiwatarwa ba a aiwatar da su ba sakamakon ƙarancin sakin kuɗaɗe, alhali ana kashe makudan kuɗaɗe a wasu fannoni daban.

Ya ƙara da cewa yawancin Ma’aikatun da suka zo kare kasafinsu, babban ƙorafinsu shi ne rashin sakin kuɗaɗe.

Da yake mayar da martani, Babban Akanta na Tarayya, Shamsudeen Ogunjumi, ya ce yawan bayar da kwangila ba tare da tabbacin samuwar kuɗi ba da wasu Ma’aikatu ke yi ne ya haddasa wannan matsala. A cewarsa, hakan ne ya sa aka bayar da umarnin hana Ma’aikatu bayar da kwangila idan babu kuɗin da za a aiwatar da su.

Ya bayyana cewa duk da ƙalubalen da aka fuskanta a tsarin biyan kuɗi na bai ɗaya, waɗannan matsalolin ba a hango su ba tun da farko, amma ana aiki tukuru domin gyara su don samun sauƙin aiki.

Ya ce:“Eh, a matsayina na Babban Akanta na Tarayya, ana sa ran ofishina ya rika sakin kuɗaɗe ga hukumomin da suka dace a kan lokaci. Amma hakan zai yiwu ne kawai idan kuɗin yana nan, domin dole ne in samu kuɗin kafin in iya raba shi.”

Ya kuma danganta matsalar da yadda tsarin Ways and Means da ake amfani da shi a baya wajen samun kuɗaɗen tallafi ya daina aiki, domin kare lafiyar tattalin arziƙin ƙasa.

COV: Bashir Mayere

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara