Ilimi
Tinubu Ya Umaurci Matawalle Ya Koma Kebbi a Cigaba da Kokarin Kubutar da Daliban da Aka Sace
Daga Bello Wakili
Shugaba Bola Tinubu ya umurci Ministan Tsaro, Alhaji Bello Matawalle, da ya koma Jihar Kebbi biyo bayan sace dalibai ’yan mata 24 a jihar.
An umurci Matawalle, wanda tsohon gwamnan Jihar Zamfara ne, da ya zauna a jihar domin sa ido kan ƙoƙarin da ake yi na kubutar da ɗaliban da aka sace.
’Yan bindiga sun sace ɗalibai mata 24 na Makarantar Sakandare ta ’Yan Mata da ke garin Maga, Jihar Kebbi, da misalin ƙarfe 4 na asubar ranar Litinin.
Matawalle, wanda ake sa ran zai isa Birnin Kebbi a ranar Juma’a, ya samu ƙwarewa wajen fuskantar matsalar ’yan fashi da garkuwa da mutane a lokacin da yake gwamnan Jihar Zamfara daga shekarar 2019 zuwa 2023.
Idan za a iya tunawa ranar 26 ga watan Fabrairun 2021, ’yan bindiga sun sace ɗalibai mata 279 da ke tsakanin shekaru 10 zuwa 17 a Makarantar Sakandare ta Kimiyya ta ’Yan Mata da ke Jangebe, a Jihar Zamfara. ’Yan bindigar sun saki dukkan waɗanda suka yi garkuwa da su a ranar 2 ga Maris 2021.
Shugaba Tinubu ya ɗage tafiyarsa da aka shirya zuwa Johannesburg, Afrika ta Kudu, da kuma Luanda, na kasar Angola, domin ya jira bahasin halin da ake ciki game da ’yan matan makarantar da aka sace a Kebbi da kuma harin da aka kai wa masu ibada na Cocin Christ Apostolic da ke Eruku, Jihar Kwara.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai22 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
