Labarai
Gwamna Idris Ya Amince da Kafa Kwamitin Binciken Aikin Gidan Gwamnan Kebbi da Otal da Aka Yi Watsi da su a Kaduna
Gwamnan Jihar Kebbi, Dokta Nasir Idris, ya amince da kafa kwamitin ƙwararru domin bincike kan halin da ake ciki na aikin gina Gidan Gwamnan Jihar Kebbi da Otal da ke Kaduna, waɗanda aka daɗe da yi wa watsi da su.
An sanar da wannan amincewa ne ta hannun Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Yakubu Bala Tafida, sakamakon damuwar da ake nuna kan aikin da aka fara tun a zamanin mulkin soja amma aka bari ya lalace ba tare da kammalawa ba.
An ɗora wa kwamitin alhakin, daga cikin sauran ayyuka, tantance matsayin shari’a na aikin, da kuma gano ko kamfanin da aka ba kwangilar ya yi sulhu da Gwamnatin Jihar Kebbi kamar yadda tsohon Babban Lauyan Gwamnati ya taɓa ba da shawara bayan soke kwangilar.
Haka kuma, kwamitin zai binciki halin da aikin ke ciki a yanzu tare da gano dalilan da suka jawo watsi da aikin.
Sauran muhimman sharuɗɗan aikin kwamitin sun haɗa da gano yanayin da ya kai ga soke kwangilar da gwamnatin jihar ta yi, da kuma tantance adadin kuɗaɗen kwangilar da aka fara bayarwa da kuma waɗanda aka sake bitar su.
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na Jihar Kebbi, Alhaji Yakubu Ahmed Birnin Kebbi, ne shugaban kwamitin. Sauran mambobin sun haɗa da Mai Ba Gwamna Shawara kan Bin Ka’idoji (Due Process), Surajo Garba Bagudo; Babban Sakatare a Ma’aikatar Filaye da Gidaje, Ahmad Umar Yarima; da Daraktan Tsare-Tsare da Gina Gine-gine a Ma’aikatar Ayyuka, yayin da Daraktan EXCO, Kabiru Hassan Wasagu, zai kasance Sakataren kwamitin.
An bai wa kwamitin wa’adin makonni biyu domin kammala aikinsa tare da miƙa cikakken rahoto ga Gwamnatin Jihar Kebbi.
REL SANI DUTSINMA
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
-
Labarai2 days ago2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro
