Labarai
Gwamnan Niger Ya Amince da Ɗage Haramcin Babura da Keke Napep a Minna
Gwamnan Jihar Niger, Mohammed Umar Bago, ya amince da ɗage gaba ɗaya haramcin zirga-zirgar babura da keke napep a cikin birnin Minna tsakanin ƙarfe 8:00 na dare zuwa 6:00 na safe.
An bayyana wannan mataki ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Niger, Alhaji Abubakar Usman, ya fitar ga manema labarai, inda ya ce an yanke shawarar ne bayan cikakken bita kan halin tsaro da ake ciki a Minna, bisa ƙwararan shawarwarin Kwamitin Tsaron Jihar.
Ya ce ɗage haramcin na nuni da ingantuwar tsaro mai ɗorewa a birnin Minna, yana mai jaddada cewa sanya haramcin tun farko mataki ne na kariya wanda ya cim ma manyan manufofinsa na rage ayyukan ta’addanci da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Alhaji Abubakar Usman ya yabawa ƙwazon jami’an tsaro da jajircewarsu, tare da jin daɗin yadda mazauna Minna suka nuna haƙuri, fahimta da haɗin kai a tsawon lokacin da aka sanya takunkumin zirga-zirga.
Sai dai ya tabbatar wa al’ummar Jihar Niger cewa gwamnatin Gwamna Mohammed Umar Bago na nan daram wajen tabbatar da tsaro da walwalar jama’a, yana mai cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da aiki kafada da kafada da hukumomin tsaro domin bibiyar al’amura da kuma kare zaman lafiya da tsaro a faɗin birnin.
Alhaji Abubakar Usman ya kuma yi kira ga masu babura da keke napep, da kuma sauran jama’a, da su gudanar da harkokinsu cikin bin doka, tsari da ladabi, kasancewar an umurci jami’an tsaro da su ci gaba da kasancewa cikin shiri tare da tsaurara bin dokokin zirga-zirga da na tsaro da ke aiki.
PR Aliyu Lawal
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
