Labarai
Gwamnatin Jihar Kwara Ta Kaddamar Shirin Bada Horo Ga Manoma
Gwamnatin Jihar Kwara ta kaddamar da jerin zirga-zirgar horaswa da gina ƙwarewa ga manoma da makiyaya a dukkanin ƙananan hukumomi 16 na jihar, domin ba su damar rungumar ingantattun hanyoyin kiwon dabbobi masu ɗorewa da za su aiwatar a gonakinsu.
Da take jawabi yayin horaswar da aka gudanar a Ilorin, Kwamishiniyar Ci gaban Kiwo ta Jihar Kwara, Hajiya Oloruntoyosi Thomas, ta ce shirin ziyarar horaswar na da nufin faɗaɗa ilimin manoman jihar kan tsarin kiwo na zamani (ranching) da kuma ƙara yawan amfanin da ake samu a ɓangaren kiwo.
Ta bayyana cewa ziyarar karatu da shirin bayar da horo an tsara su ne domin daidaitawa tare da zurfafa aiwatar da kyawawan dabarun kiwo a gonakin mahalarta.
Kwamishiniyar ta tabbatar wa mahalarta cewa Ma’aikatar na mayar da hankali ne wajen gina masana’antar kiwo ta zamani wadda za ta iya yin gogayya a kasuwa, tare da tallafa wa samar da abinci da bunƙasa tattalin arziki.
Hajiya Thomas ta shawarci mahalarta da su amfana da ilimin da suka samu a yayin ziyarar domin inganta yadda gonakinsu ke aiki, ta yadda za su cim ma gagarumar riba da ci gaba.
A nasa jawabin, Daraktan Gudanarwa na ɗaya daga cikin gonakin masu zaman kansu da aka ziyarta, Mista Tony Jibunoh, ya buƙaci mahalarta da su rungumi sabbin ƙirƙire-ƙirƙire da fasahohin zamani, domin ƙara inganci a gonakinsu, haɓaka amfanin da ake samu, da kuma tabbatar da wadatar abinci.
A jawabansu daban-daban, wasu daga cikin manoman sun bayyana ziyarar a matsayin abin buɗe ido, inda suka yabawa gwamnatin jihar bisa sauƙaƙa shirya wannan shirin.
Sun ƙara da cewa ziyarar ta ƙara musu fahimta kan kiwo na zamani, tare da gabatar musu da sabbin fasahohi da za su inganta aikin gonakinsu gaba ɗaya.
Mahalarta sun samu horaswa kan ingantattun dabarun kiwon dabbobi, kula da jin daɗin dabbobi, kula da ciyawa da abinci, sarrafa shara, kiwo da haifuwa.
ALI MUHAMMAD RABIU
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
