Labarai
Fitattun ’Yan PDP Sun Koma APC a Zamfara Gabanin Zaɓen 2027
Gabanin babban zaɓen 2027, Alhaji Bello Mohammed Nakwada, ƙanen Sakataren Gwamnatin Jihar Zamfara kuma wanda ɗaya daga cikin masu tallafa wa kamfen ɗin Gwamna Dauda Lawal a zaɓen 2023, ya fice daga jam’iyyar y (PDP) mai mulki a jihar zuwa (APC).
Nakwada ya sanar da sauya sheƙarsa ne a ranar Talata, inda ya bayyana cewa tsauraran matakai, rashin adalci da kuma rashin dimokiraɗiyyar cikin gida a jam’iyyar PDP a Zamfara ne suka tilasta masa ɗaukar wannan mataki.
A cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaran APC a Jihar Zamfara, Yusuf Idris Gusau, ya fitar, an ambato Nakwada yana bayyana nesantarsa daga gwamnatin PDP da ke mulkin jihar, ciki har da Gwamna Dauda Lawal da kuma ɗan’uwansa babba, Abubakar Muhammad Nakwada, wanda shi ne Sakataren Gwamnatin Jihar a halin yanzu.
Haka kuma, Hassan Idris Gusau, wanda ya taɓa neman kujerar shugaban ƙaramar hukumar Gusau a ƙarƙashin PDP a zaɓen ƙananan hukumomi da ya gabata, shima ya sauya sheƙa zuwa APC.
An tarbi dukkanin masu sauya sheƙar, tare da wasu daga cikin magoya bayansu, a birnin Abuja ta hannun ministan kasa a Ministan Tsaro, Dokta Bello Mohammed Matawalle.
Da suke jawabi daban-daban, Nakwada da Hassan Idris sun yabawa haɗin kai da ɗorewar tsari a cikin APC, inda suka bayyana jam’iyyar a matsayin wadda ke bai wa mambobinta daidaito da mutunci. Sun danganta hakan da irin salon jagoranci na manyan jagororin jam’iyyar, ciki har da Dokta Bello Mohammed Matawalle da kuma Sanata mai daraja Abdul’aziz Yari Abubakar.
Sun kuma yi alƙawarin cikakken biyayya ga APC da shugabancinta, tare da tabbatar da cewa magoya bayansu da abokan tafiyar siyasa sun amince da sauya sheƙar, kuma suna shirye su yi aiki tukuru domin nasarar jam’iyyar.
Da yake karɓar sababbin mambobin, Dokta Matawalle ya nuna farin cikinsa kan shigowarsu APC, inda ya ba su tabbacin cikakken haɗewa cikin jam’iyyar tare da samun dukkan haƙƙoƙi, gata da fa’idodin da mambobin APC ke samu.
Ya kuma buƙace su da su ƙarfafa magoya bayansu su shiga rajistar dijital ta APC da ake ci gaba da gudanarwa, yana mai bayyana wannan tsari a matsayin muhimmin ginshiƙi wajen ƙarfafa jam’iyyar gabanin zaɓuka masu zuwa.
REL/AMINU DALHATU
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
