Connect with us

Labarai

Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan PDP a Gombe Ya Karɓi Katin APC

Published

on

Daga Hudu Shehu.

Tsohon ɗan takarar gwamnan Jihar Gombe a ƙarƙashin jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Alhaji Jamilu Gwamna, ya yaba wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa ƙaddamar da tsarin rajistar dijital da sake tantance katin mambobin jam’iyyar APC, yana mai bayyana matakin a matsayin ginshiƙi na nasarar jam’iyyar a zaɓen 2027.

Alhaji Jamilu Gwamna ya bayyana hakan ne a rumfar zaɓensa da ke unguwar Jeka-da-Fari a birnin Gombe.

Ya ce, baya ga ƙarfafa yawan mambobin jam’iyyar a faɗin jihar ta hanyar rajista da sake tantancewa, ana iya amfani da wannan tsari a matsayin ma’adanar bayanai wajen taimakawa magance matsalar rashin tsaro.

Alhaji Jamilu Gwamna ya kuma yi alƙawarin ƙara wayar da kan jama’a tare da ƙarfafa mambobi su yi rajista da sake tantance katinsu, yana mai jaddada aniyarsa ta ƙarfafa jam’iyyar APC a Jihar Gombe gabanin zaɓuka masu zuwa.

A cewarsa, jam’iyyar APC ta ci gaba da kasancewa mai ƙarfi da cikakken damar lashe zaɓe, sakamakon shirye-shiryen da suka shafi walwalar al’umma da wakilan jam’iyyar ke aiwatarwa a matakai daban-daban na gwamnati.

Da yake jawabi, Shugaban jam’iyyar APC na mazabar Jeka-da-Fari, Alhaji Abubakar Dan-Gombe, ya yabawa Jamilu Gwamna bisa karɓar katin zama mamba da kuma sake tantancewarsa, inda ya ce hakan zai taimaka wajen ɗaga martabar jam’iyyar da kuma sanya ta a sahun nasara.

An ƙaddamar da tsarin rajistar dijital da sake tantance katin mambobin APC ne kwanan nan ta hannun Gwamnan Jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya, domin ƙara yawan mambobin jam’iyyar da kuma inganta tsarin gudanarwarta, gabanin babban zaɓen 2027.

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara