Labarai
Gwamnatin Jigawa Za ta Biya Diyar Naira Miliyan 74 ga Wadanda Aikin Sansanin Soji na Yargaba ya Shafa
Daga Usman Muhammad Zaria
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da biyan Naira Miliyan 74 a matsayin diyya da kuma sake matsuguni ga mutanen da aikin gina sansanin sojojin Yargaba ya shafa.
A cikin wata sanarwa da kwamishinan labarai na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ya mika wa manema labarai, ya ce amincewar ta shafi diyya da sake matsugunin mutane 229 da aikin ya shafa.
Ya ce, Majalisar ta kara amincewa da sake maida mutanen da abin ya shafa wajen rarraba filaye na sake matsuguni da gonaki a wuraren da aka tanada, bisa ka’idoji da manufofin gwamnati kan sauyin wuri da sake matsuguni.
Sagir Musa ya kara da cewa wannan matakin na nuna jajircewar gwamnatin jihar wajen tabbatar da cewa al’ummar da ayyukan gine-ginen gwamnati suka shafa ana kula da su yadda ya kamata, ana basu diyya bisa adalci, sannan a sake musu matsuguni cikin kima.
Har ila yau, ya ce Majalisar ta sake jaddada cewa tsarin biyan diyya da sake matsuguni zai kasance a bude kuma bisa adalci, yayin da ma’aikatun gwamnati, sassa da hukumomi za su tabbatar da aiwatar da shi yadda ya dace bisa tsarin doka.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
