Connect with us

Labarai

HARIN MASALLACIN KANO: Obi Ya Ziyarci Wadanda Ke Asibiti

Published

on

 

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour (LP) a zaben 2023, Peter Obi, ya ziyarci wadanda kona masallacin Kano ya shafa.

 

Dan takarar shugaban kasa na LP ya ziyarci wadanda abin ya shafa a asibitin kwararru na Murtala Mohammed inda suke karbar kulawa.

 

Ya ce, “Wannan abu ne mai ban tsoro kuma ya kasance abin la’akari sosai. Abin bakin ciki ne wannan na iya faruwa a kasarmu a yau. Ba wanda zai iya cewa dalilin da ya sa wannan yaron zai iya yin irin wannan abu ga danginsa da sauran al’umma.

 

“Muna ci gaba da yin Allah wadai da irin wannan aika-aikar a kan mutane. Dalilina na zuwa nan shi ne don in nuna cewa hadin kai da goyon baya a cikin kulawar su ta wata hanya da kuma masu kula da asibitoci a cikin abin da suke yi da kuma sake yin Allah wadai da wannan mummunan kisa na rashin hankali.”

 

Peter Obi ya jajanta wa gwamnati da al’ummar Kano, ya kuma bukaci ‘yan Nijeriya da su hada kai don yakar irin wannan rashin hankali.

 

Idan za a iya tunawa Rediyon Najeriya ya bada labarin cewa harin ya samo asali ne sakamakon rikicin da ya barke tsakanin dangi kan rabon gado ya haifar da bakin ciki da mutuwar mutane da dama a unguwar Larabar-Albasawa da ke wajen garin Gezawa, hedikwatar karamar hukumar Gezawa ta jihar Kano.

 

Abdullahi Jalaluddeen Kano/Wababe

Labarai

Labarai1 day ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai1 day ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai6 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara