Labarai
Shugaba Tinubu Ya Jajantawa Al’ummar Jihar Neja Bisa Iftila’in Fashewar Tankar Mai
Shugaba Bola Tinubu ya bayyana alhininsa kan fashewar tankar mai da ta yi sanadin mutuwar mutane sama da 80 tare da jikkata wasu da dama a jihar Neja.
Wata sanarwar mai dauke da sa hannun mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Mista Bayo Onanuga, ta ce shugaba TTinubu ya yi jimamin afkuwar lamarin, ya kuma jajantawa iyalan wadanda abin ya shafa, da kuma gwamnati da al’ummar jihar Neja.
Shugaban ya bayyana takaicinsa duba da yadda mafi yawan wadanda lamarin ya rutsa da su, masu kokarin dibar mai ne daga tankar man da ta fadi.
Shugaban ya bayar da umarnin ba da cikakkiyar kulawa ga wadanda suka jikkata, sannan ya umarci hukumomin tsaro da na kiyaye hadurra da su aiwatar da matakan dakile afkuwar irin wannan lamari.
Ya shawarci jama’a da su yi taka-tsan-tsan tare da kaucewa tunkarar wuraren da aka samu irin wadannan hadurra, musamman ma na motocin da ke dauke da man fetur.
Shugaban ya umarci hukumar wayar da kan jama’a ta kasa da ta kaddamar da gangamin wayar da kan jama’a game da munanan hadurra da kuma illolin da ke tattare da debo man fetur daga tankar mai.
Daga Bello Wakili
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai7 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai1 day agoGwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
