Labarai
NDLEA Ta Kama Sama Da Tan 2 Na Miyagun Kwayoyi Da Mutane 929 A Jihar Kwara
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) reshen jihar Kwara, ta kama tan 2 da digo 6 na miyagun kwayoyi, tare da kama mutane 929 tsakanin watan Janairu zuwa Disamban wannan shekara.
Kwamandar hukumar ta NDLEA a jihar Kwara, Fatima Popoola ce ta bayyana hakan yayin da take yi wa manema labarai karin haske kan nasarorin da hukumar ta samu a Ilori.

Ta ce daga cikin wadanda ake zargin 839 maza ne yayin da 90 kuma mata ne.
Misis Popoola ta ce magungunan da aka gano sun hada da, tabar wiwi da kwayar Tramadol, da diazapam, da methamphetamine, da maganin tari na ruwa da hodar ibilis da sauransu.
Ta ce tabar wiwi da ke kan gaba a jerin kwayoyin ta kai nauyin kilogiram miliyan daya da rabi.
Ta yi nuni da cewa, yayin wani aikin hadin gwiwa da hukumar ta yi cikin gaggawa, ta kama masu shaye-shaye 185, wadanda aka fadakar da su illar shaye-shaye, tare da ba su shawarwari, aka kuma maida su ga iyalansu.

Misis Popoola ta ci gaba da cewa, hukumar tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar, ta fara aiwatar da shirin gwajin magunguna kan sabbin dalibai 261 na jami’ar jihar Kwara.
Kwamandar hukumar ta NDLEA ta yabawa kokarin gwamnatin jihar da sauran jami’an tsaro bisa tallafawa ayyukansu.
Ta shawarci iyaye da su kasance masu sa ido kan al’amuran ‘ya’yansu don kaucewa tu’ammali da miyagun mutane.
Misis Popoola ta bukaci gwamnatin jihar da ta taimaka wa hukumar da karin motocin aiki tare da kammala ginin cibiyar gyaran dabi’u domin saukaka ayyukansu.
Ta kuma yi kira ga jama’a da su taimaka wa hukumar da bayanai kan ayyukan masu safarar miyagun kwayoyi domin samun nasara.
Ali Muhammad Rabi’u
-
Labarai4 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai5 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai2 days agoHukumar Kula da Kogin Benuwe ta Dauki Matakin Yashe Laka da Yashi da ke Barazana ga Noman Rani
-
Labarai6 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai3 days agoGwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu
-
Labarai5 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai5 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
-
Labarai4 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
