Connect with us

Labarai

NDLEA Kano Ta Kama Mutane 1,389 a 2025

Published

on

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA), reshen Kano, ta samu gagarumar nasara a shekarar 2025, inda ta kama mutane 1,389 da ake zargi da laifukan da suka shafi miyagun ƙwayoyi, tare da kwace kilogiram 7,773.06 na nau’o’in miyagun ƙwayoyi daban-daban, ciki har da tabar wiwi, da ta aljannu da kokin da a farci kasa da kuma ƙwayoyin maye na kwakwalwa.

Wadannan alkaluma, kamar yadda Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Sadiq Muhammad Maigatari, ya bayyana, sun nuna irin gagarumar nasarar da rundunar ta samu ƙarƙashin jagorancin Kwamanda CN D.Y. Lawal wajen yaƙi da fatauci da shan miyagun ƙwayoyi a faɗin jihar Kano.

Daga cikin waɗanda aka kama, 1,346 maza ne yayin da mata 43 ne. Haka kuma rundunar ta samu hukunci 141 a kotu, lamarin da ya zama darasi ga masu shirin aikata irin waɗannan laifuka, inda manyan dillalan miyagun ƙwayoyi guda huɗu suka samu hukuncin da ya kai shekaru 33 a gidan yari gaba ɗaya.

Baya ga kamen mutane da gurfanarwa, rundunar ta kuma samu nasarar kwace wani gida da aka mallaka ta hanyar kudaden miyagun ƙwayoyi, tare da kwace wasu kadarori biyu na wucin gadi, yayin da shari’o’i 133 ke ci gaba da sauraro a Kotun Tarayya.

A fannin gyara da wayar da kan jama’a, NDLEA Kano ta ba da muhimmanci ga shirin farfaɗo da masu shaye-shaye da hulɗa da al’umma. Mutane 94 sun kammala shirye-shiryen gyaran hali na musamman, yayin da mutane 1,009 (ciki har da mata 28) suka samu shawarwari na gajeren lokaci.

Rundunar ta gudanar da kamfe 254 na yaƙi da miyagun ƙwayoyi a makarantu, kasuwanni da cibiyoyin al’umma, inda ta kai saƙon wayar da kai ga mutane 86,939 (maza 41,225 da mata 45,714) ta hanyar taruka da shirye-shiryen wayar da kai kan illolin shan miyagun ƙwayoyi.

Haka kuma, hukumar ta gudanar da gwaje-gwajen shan miyagun ƙwayoyi 527, inda mutane 64 suka nuna alamun shan ƙwayoyi. Daga cikin waɗanda aka yi wa gwajin har da sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma, domin jaddada muhimmancin shugabanci mara alaƙa da miyagun ƙwayoyi a jihar.

A cikin haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro da na sa ido, NDLEA Kano ta miƙa wasu shari’o’i ga ’Yan Sanda, Sojoji, DSS, NAFDAC da EFCC, waɗanda suka shafi laifuka irin su safarar makamai, ’yan bindiga, damfara, sata da kuma magungunan bogi.

Khadijah Aliyu

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara