Connect with us

Labarai

Jami’an NDLEA A Kano Sun Kama Wata Tirela Dauke Da Miyagun Kwayoyi Daga Legas

Published

on

Jami’an Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) shiyar Kano sun kama kwalabe 8,000 na Akuskura, wani hadin ganyen magani da ake zargin na dauke da miyagun kwayoyi, tare da sinki 48 na tabar wiwi.

Mai magana da yawun hukumar ta NDLEA a Kano, Sadik Muhammad Maigatari, ya bayyana cewa an cafke wani mutum mai shekaru 37 mai suna Ali Muhammad da ke da alaka da wannan laifi.

Ya bayyana cewa an kama kayan ne a Gadar Tamburawa, kan hanyar Zariya zuwa Kano, lokacin da jami’an suka dakatar da wata tirela dauke da kaya, da ta taso daga Legas zuwa Maiduguri.

Sadik ya kara da cewa, tirelar wacce take makare da Keke Napep, inda aka boye kayan a tsakanin kekunan da kuma karkashin tirelar, a wani rami na musamman da aka kera da katako domin boye miyagun kwayoyin.

Jami’an  sun gano kayan da aka boye ta hanyar bincike mai zurfi da kuma bayanan sirri.”

Ya ce yanzu haka ana tsare da wanda ake zargi tare da kayan da aka kama, inda ake ci gaba da bincike da gwaje-gwaje domin tantance sinadaran da ke cikin hadin da kuma gano sauran abokan huldarsa.

Sadik ya kara da cewa, kwamandan hukumar shiyar  Kano, A. I. Ahmad, ya yaba da kokarin jami’ansa, tare da nuna godiya ga goyon bayan shugaban hukumar, Brig. Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya), wanda ke karfafa jami’an wajen fatattakar masu safarar miyagun kwayoyi.

Hukumar ta kuma shawarci al’umma da su kasance masu sa ido, tare da bayar da rahoton duk wasu kaya ko aiki da ake zargin na da nasaba da miyagun kwayoyi ga ofishin NDLEA mafi kusa ko kuma ga sauran jami’an tsaro.

 

Daga Khadijah Aliyu

Labarai

Labarai1 day ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai1 day ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara