Labarai
An Ciro Kullin Hodar Iblis 57 A Cikin Wani Mutumt Ta Hanyar Tiyata
Hukumar sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta kasa NDLEA ta ce an yi wa wani mutum mai shekara 59 tiyata domin ciro sunƙin hodar ibilis 57 cikin guda 81 da ya haɗiye kwanaki bakwai da suka gabata a Addis Ababa da ke kasar Habasha.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi ya fitar, ta ce an kama mutumin ne a lokacin da ake tantance fasinjoji bayan isar su filin jirgin sama na Murtala Muhammad daga Habasha a ranar 26 ga watan da ya gabata.
Kakakin hukumar ya ce bincike ya gano cewa mutumin wanda ya yi iƙirarin ɗan kasuwa ne a yankin Oshodi da ke jihar Lagos, ya tafi Addis Ababa inda ya haɗiyi sunƙi 81 na hodar ibilis ɗin, daga bisani kuma ya hau jirgi zuwa Beirut da ke kasar Lebanon domin kaiwa a kan kuɗi dala 3000.
Ya kuma ce binciken nasu ya nuna cewa mutumin bai samu shiga ƙasar ba saboda kuɗin hannunsa ba su kai dala 2,000 ba da ake buƙata kafin shiga ƙasar ta Lebanon, wanda ya sa aka mayar da shi Addis Ababa inda ya yi yunƙirin fitar da miyagun ƙwayoyin amma ya kasa, daga nan kuma ya dawo Najeriya inda suka yi nasarar cafke shi.
Femi ya ƙara da cewa bayan kwanaki 5 ƙarƙashin sa idon hukumar a asibitin koyarwa na Jami’ar Jihar Lagos, mutumin ya yi kashin sunƙin hodar ibilis guda 24, inda daga bisani saboda gujewa kamuwa da rashin lafiya, aka yi masa tiyata domin cire sunƙi 57 da suka rage bayan uwargidansa da ɗan’uwansa sun amince da yin hakan.
bbc
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
