Labarai
Muna Jaje Ga Masautar Zazzau – Manjo Janar Bello
Kwamandan makarantar horas da sojoji dake Zaria, Manjo Janar Ahmadu Bello Mohammed ya yi alkawarin inganta dangantakar da ke tsakanin makarantar da majalisar masarautar Zazzau.
Ya bayyana haka ne lokacin da ya kai wa mai martaba Sarkin zazzau Malam Ahmed Nuhu Bamalli ziyarar ban girma a fadar sa dake Zaria.
Manjo Janar Ahmadu Bello, wanda ya bayyana ziyarar a matsayin wani sabon babi a dangantakar daje tsakanin makarantar horas da kuratan da masarautar ta zazzau ya yi alkawarin bunkasa dangantakar dake tsakanin su,ya kuma bayyana cewa ya kai ziyarar ce domin neman albarka da hadin kan majalisar masarautar ta zazzau.
Kwamandan ya kuma mika ta’aziyar makarantar horas da kuratan sojojin ga masarautar ta zazzau bisa rasuwar daya daga cikin yan majalisar masarautar, Alhaji Rilwanu Yahaya Fate,Sarkin Yaki zazzau da ya rasu kwanan nan.
Da ya ke maida jawabi, mai martaba Sarkin zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli ya gode wa Kwamandan bisa ziyarar, ya kuma yi alkawarin baiwa makarantar ta Dapo duk goyon baya da hadin kai da suke bukata domin sauke nauyin dake kan su.
Mai martaban ya kara da cewa za a gudanar da tsare-tsaren da suka kamata domin daidaita batutuwan dake masarautar ta zazzau da masarautar horas da kuratan sojojin.
Haliru Hamza
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
