Connect with us

Labarai

Rundunar Operation Fansan Yamma Ta Raba Takin Zamani Ga Monoma A Karamar Hukumar Tsafe

Published

on

A wani yunkuri na kokarin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Arewa maso Yamma da wasu sassan Arewa ta  Tsakiya, Kwamandan Rundunar Operation Fansan Yamma, Manjo Janar O.O. Soyele, ya raba buhunan taki 200 ga manoma a karamar hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara.

Wata sanarwa da jami’in yada labarai na rundunar Kyaftin David Adewusi, ya fitar ta bayyana cewa wannan tallafi an yi shi ne da nufin karfafa amfanin gona da inganta rayuwar al’umma a yankin.

Janar Soyele wanda ya sami wakilcin Kwamandan Sashen Kayayyakin Aiki na Rundunar, Birgediya Janar Nkemakolam Mbaka, ya mika buhunan takin ga Sarkin Tsafe, Alhaji Abubakar Muhammad Bawa, a matsayin wani bangare na shirin kyautata hulɗa tsakanin sojoji da al’umma,  na Hedikwatar Tsaro.

Janar Soyele ya bayyana cewa wannan shiri na hanyar sulhu ba tare da amfani da karfi ba an yi shi ne domin bunkasa harkar noma, karfafa hulɗar sojoji da al’umma, da kuma ƙarfafa manoma su koma gona, a daidai lokacin da ake gudanar da samamen kawar da barazanar tsaro a yankunan noma.

Kwamandan ya kuma gode wa Sarkin Tsafe, gwamnati da al’ummar Jihar Zamfara bisa goyon bayan da suke bayarwa wajen yaki da ta’addanci da ’yan bindiga.

Ya shawarci manoma da su yi amfani da takin yadda ya kamata domin samun karin amfanin gona.

 

A nasa jawabin, Sarkin Tsafe, Alhaji Abubakar Muhammad Bawa, ya gode wa Kwamandan Rundunar bisa abin da ya bayyana a matsayin taimakon da ya zo a kan gaba. Ya ce wannan kyauta za ta inganta samar da abinci da kuma kyautata rayuwar manoma, tare da tabbatar da ci gaba da goyon baya ga sojoji.

Taron ya samu halartar shugabannin al’umma, wakilan shugaban karamar hukumar Tsafe, da kuma jama’ar garin da suka yaba da wannan shiri.

Daga Aminu Dalhatu

 

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara