Connect with us

Labarai

Hisbah Ta Kama Wani Mutum Da Ke Yunkurin Safarar Mata 12 A Kano

Published

on

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da safarar mutane tare da mata 12 a wata tashar mora da ke kan titin  Zaria.

Rahotanni sun bayyana cewa mutumin, wanda ba a bayyana sunansa ba, an kama shi ne  yana yunkurin safarar matan  zuwa Legas.

Mataimakin Kwamandan Janar na Hisbah, Sheikh Mujahideen Aminuddeen, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa, inda ya ce jami’an hukumar karkashin jagorancin jami’in da ke kula da tashoshin mota, Muhammad Bashir ne suka cafke wanda ake zargin, wanda dan asalin jihar Borno ne.

Bincike na farko ya nuna cewa an shirya safarar matan ne zuwa kasashen waje ta hanyar Legas, inda za su bi ta Jamhuriyar Benin da kumGhana, sannan daga bisani a kaisu Saliyo.

Ana zargin wanda aka kama da tsara musu takardun izinin shiga kasar Saudiyya domin neman aikin yi.

A cewar Hisbah, matan sun bayyana yayin bincike cewa kowannensu ta riga ta biya Naira miliyan ɗaya da rabi (₦1.5m) a matsayin kafin alkalami, tare da yarjejeniyar cewa za su biya sauran kudin bayan sun samu ayyukan yi a ƙasar da za a kaisu.

Hukumar ta nuna damuwa cewa irin wannan kudi mai yawa na iya zama jari domin dogaro da kai a gida.

Aminuddeen ya ce matan sun bambanta a shekaru, ciki har da wadda ta kai shekara 50, wasu biyu ’yan shekara 23, wasu biyu kuma ’yan shekara 20, yayin da sauran mafi yawan su ’yan shekara 15 ne kacal. Sun fito ne daga jihohin Katsina, Kano, Borno, Jigawa da Zamfara.

Wannan abin takaici ne,” in ji shi. “Kudin da suka biya ya isa su fara sana’a mai kyau a jiharsu. Amma suka zabi su sa kansu cikin hadarin irin wannan tafiya.” Ya bukaci iyaye da su ja hankalin ’yayansu game da irin waɗannan lamurra masu hadari.

Kwamandan ya gargadi cewa ko da sun samu takardar izinin shiga Saudiyya, babu tabbacin aikin da za su yi a can. “Idan kuma an kasa samun visa, za a karkatar da su zuwa Saliyo. Wannan lamari hadari ne kuma abin takaici,” In ji shi.

Daga karshe, hukumar Hisbah ta mika wanda ake zargi da matan ga Hukumar Yaki da Safarar Mutane ta Kasa (NAPTIP) domin gudanar da cikakken bincike da daukar matakan da suka dace.

 

Daga Khadijah Aliyu 

 

 

Labarai

Labarai20 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai22 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara