Connect with us

Labarai

Hukumar NSCDC Ta Kama Masu Satar Kayayyakin Lantarki A Kano

Published

on

Hedkwatar Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (NSCDC) a Jihar Kano ta kama mutane shida da ake zargi da lalatawa da kuma satar kayayyakin wutar lantarki a jihar.

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, SC Ibrahim Idris Abdullahi, ya bayyana hakan ga manema labarai a madadin kwamandan jihar, Shafi’u Abdulmumini.

Ya ce an cafke mutanen ne bayan samun sahihan bayanan sirri daga kungiyar sa-kai ta Hayin Da’e, da ke Hotoro, a ƙaramar hukumar Tarauni.

Abdullahi ya bayyana cewa an kama mutanen da wayoyin lantarki da aka lalata, waɗanda ake zargin sun cire ne daga wata na’urar tiransifoma da ke yankin.

Akasarin wadanda aka kama mazauna yankin ne da aka yi aika-aikar, wadanda  shekarunsu suka kama da 18 zuwa 28.

Bincike na farko ya nuna cewa waɗanda ake zargin sun dade suna addabar mazauna Hayin Da’e, Farawa Kwanar Yashi, da Hotoro, ta hanyar fasa-kwauri, sata, da kuma lalata kayayyakin wutar lantarki,” in ji Abdullahi.

Kakakin NSCDC ya ce an riga an samu shaidar furuci daga hannun waɗanda ake zargin, yayin da bincike ke ci gaba domin cafke sauran abokan harkar su.

Ya tabbatar da cewa za a gurfanar da su a gaban kotu bayan kammala bincike.

Shugaban hukumar, Shafi’u Abdulmumini, ya jaddada aniyar NSCDC wajen kare muhimman kayayyaki da kuma tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a jihar.

Haka kuma ya bayyana cewa an ƙara tsauraran ayyukan sintiri da sa ido a duk fadin Kano domin masu aikata sauran laifuka.

Hukumar ta kuma yaba wa ‘yan sa-kai bisa bayanan sirri da suka bayar, wanda ya taimaka wajen kama batagarin, tare da kira ga al’umma su ci gaba da kasancewa masu lura da tsaro, da kuma bai wa  jami’an tsaro hadin kai domin kawar da aikata laifuka a unguwanninsu.

 

ABDULLAHI JALALUDDEEN

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara