Ilimi
UNICEF Da EU Sun Horas Da Malaman Makarantun Firamare A Jigawa Kan Manhajar Koyarwa
Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF),da Kungiyar Tarayyar Turai (EU), tare da hadin gwiwar Hukumar Ilimi ta Firamare ta Jihar Jigawa(SUBEB) sun horas da masu kula da yara (caregivers) su 402 daga kananan hukumomi goma a jihar Jigawa.
Horon wani ɓangare na aiwatar da shirin ilimantarwa da tallafawa matasa na UNICEF (EU EYE p), wanda Kungiyar Tarayyar Turai ta dauki nauyinsa, da nufin kara yawan yara maza da mata da za su rika amfana da ilimi mai inganci.
Masu kula da yaran sun samu horo kan yadda ake koyarwa ta hanyar wasa ga ɗaliban firamare na farko, da kuma amfani da manhaja da littafin koyarwa na wannan mataki na ilimi, a tsawon shekara guda.
Masu horarwar sun fito ne daga makarantu 201 a kananan hukumomi goma da aka gudanar da shirin, wadanda suka hada da Babura, Birnin Kudu, Garki, Hadejia, Jahun, Kafin Hausa, Kazaure, Kiri Kasamma, Kiyawa da Maigatari.
Shirin na ilimantarwa tare da tallafawa matasa na ƙara taimakawa gwamnatocin jihohi wajen bunƙasa damar samun ingantaccen ilimi ga yara a yankunan da ba a cika kai wa gare su ba, musamman al’ummomin makiyaya da masu buƙatar kulawa ta musamman.
Kungiyar Tarayyar Turai da Gwamnatin Tarayya sun sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna a watan Maris na 2023 domin samar da kudin gudanar da shirin.
Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, wannan shiri wanda ke cikin manyan manufofin ci gaban ɗan adam na kungiyar Tarayyar Turai, an tsara shi ne da nufin tallafawa fannin ilimi da bincike, ta hanyar faɗaɗa damar samun ilimi na zamani, da zai inganta fannin ilimi, da aiwatar da nagartattu tsare-tsare, domin kai wa ga gaci a jihohin da ke amfana da shirin.
Usman Muhammed Zaria
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai22 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
