Connect with us

Labarai

Bauchi ta kafa kwamitin Limamai da Fastoci don tabbatar da zaman lafiya a Tafawa Balewa da Bogoro

Published

on

Gwamnatin jihar Bauchi ta kaddamar da wani kwamiti na musamman na Limamai da Fastoci domin samar da hadin kai da zaman lafiya a kananan hukumomin Tafawa Balewa da Bogoro bayan wani rikici da ya barke a yanki  kwanakin baya.

Gwamnan jihar Bala Muhammad a lokacin da yake kaddamar da kwamitin a gidan gwamnati da ke Bauchi ya ce bai zai yi kasa a qwiwa ba wajen daukan matakan da su ka da ce don magance barazanar bata gari da ke kokarin wargaza zaman lafiya da tsaro a yankunan.

Bala Muhammad ya ce zaman lafiya shine ginshikin kashin bayan kowace al’umma don haka akwai bukatar a hada  malaman addini musamman Limamai da Fastoci don su suka fi kusa da Al’ummah da kuma dimbin mabiya domin wayar da kan mabiyansu kan zaman lafiya da kuma zimmar dakile sa ke barkewar rikici a kananan hukumomin biyu.

Gwamnan ya bukaci mambobin kwamitin da su yi aiki tare da masu ruwa da tsaki daban-daban don tabbatar da dorewar zaman lafiya da aka samu a kananan hukumomin biyu cikin shekaru da dama da suka gabata wanda a yanzu aka samu tsaiko  sakamakon rikicin manoma da makiyaya da ya yi sanadin asarar rayuka da dukiyoyi.

Ya bukace su da su kai rahotonin duk wani abu da su ke zargi da ya wuce ikon su ga hukumomin tsaro da abin ya shafa domin daukar matakin gaggawa.

“Ba za mu bari wani ya lalata zaman lafiyar da muka gina ba,” in ji Gwamnan. “Wannan kwamitin zai zama gada tsakanin al’umma, domin samar da fahimtar juna da zaman lafiya.”

Gwamnan ya yi bayanin ayyukan kwamitin da su ka hada da wayar da kan jama’a kan samar da zaman lafiya da tattaunawa da yin sulhu a tsakanin jama’a da nufin haka ta cimma ruwa.

Da suke mayar da martani a madadin kwamatin, Shuwagabanin kwamitin Faizu Ado Musa daga karamar hukumar Tafawa Balewa da Reverend Father Benson Bature daga karamar hukumar Bogoro sun yi alkawarin yin aiki tukuru har sai an dawo da zaman lafiya mai dorewa a yankunan.

“Za mu yi duk mai yiwa wajen sake nauyin da aka dora mana da taimakon Allah. Kuma in Allah yarda duk wadda ya ke da hannu wajen tayar da rikici a yankunanmu Allah ba zai bar shi ba”.

Shugabannin hukumomin tsaro daban-daban da suka hada da kwamishinan ‘yan sandan jihar, daraktan tsaro na jiha.  Kwamandojin soji na sama da kasa da sauransu na daga cikin waya’nda su ka halarci taron.

Cov/Alhassan.

Labarai

Labarai15 hours ago

Sauye-sauyen Da Tinubu Ya Samar Ya Haifar Da Cigaba A Jihohi – Namadi

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan matakan da...

Labarai19 hours ago

Jigawa Ta Yi Nazarin Sabbin Tsare-tsaren Masaukin Alhazai A Saudiyya

Daga Usman Muhammad Zaria Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce tana nazarin hanyoyin inganta jin daɗin alhazai...

Labarai2 days ago

Kano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400

Daga Khadijah Aliyu  Wata kotu a Jihar Kano ta bayar da umarnin lalata buhunan fulawa sama da 400 da suka...

Labarai3 days ago

Tinubu Ya Jaddada Ƙudurin Samar Da Ci Gaba A Jigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada ƙudurin gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da...

Labarai3 days ago

Shugaban Gidan Talabijin Na Katsina Abba Zayyan Ya Yi Murabus

Daga Isma’il Adamu  Babban Manajan gidan talabijin na Jihar Katsina (KTTV), Abba Zayyan, ya miƙa takardar murabus daga muƙaminsa a...

Labarai3 days ago

Namadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya kai musu...

Labarai3 days ago

Arewa Za Ta Saka Wa Tinubu Da Ruwan Kuri’a A 2027- Yari

Daga Usman Muhammad Zaria  Daraktan Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC, Sanata Abdulaziz Yari, ya ce...

Labarai3 days ago

Shettima Ya Bukaci ’Yan Najeriya Su Sake Zaben Tinubu A 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bukaci ’yan Najeriya da su goyi bayan sake zaɓen Shugaba...

Labarai4 days ago

Jigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz

Daga Usman Muhammad Zaria Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan harkokin yada labarai da wayar dan...

Labarai4 days ago

Majalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027

Daga Khadijah Aliyu  Majalisar Dokokin Jihar Kano na shirin karɓar daftarin kasafin kuɗin shekarar 2027 daga Gwamna Abba Kabir Yusuf...

Mafi Shahara