Kasuwanci
Gwamna Bago Ya Sauke Kwamishinonin Jihar Neja
Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umar Bago, ya rushe majalisar kwamishinoinsa
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labarai, Bologi Ibrahim, ya rattaba hannu kuma ya rabawa manema labarai a Minna.
A cewarsa, Gwamna Umar Bago ya bayyana wannan mataki ne a lokacin taron majalisar zartarwa ta jiha da aka gudanar a gidan gwamnati, Minna.
Gwamna Bago, wanda ya nuna godiyarsa bisa gudummawar da suka bayar wajen cigaban jihar Neja, ya yi musu fatan alheri a ayyukan da za su shiga nan gaba.
Sai dai ya bayyana cewa, ya ci gaba da aiki da Sakataren Gwamnati na Jiha, da Shugaban Ma’aikata, da Mataimakin Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnati, da kuma sauran manyan jami’ai na ofishinsa.
Daga Aliyu Lawal
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
