Labarai
Al’ummar Katsina Sun Koka Kan Yadda Shara Ta Mamaye Titin IBB
Jama’ar cikin garin Katsina sun nuna damuwa kan yadda shara ta mamaye Titin IBB, hanya mafi cunkoso a cikin garin Katsina, wadda ta tashi daga kan titin Kano zuwa kwaryar jihar, ta kai ga fadar Sarkin Katsina.
Titin IBB na da tarihi a matsayin tsohuwar hanya mafi muhimmanci a garin, wacce ta kunshi muhimman wura da suka hada da sakatariyar tarayya, gidan gwamnatin jihar Katsina, bankuna, kamfanonin inshora, makarantu, hedikwatar jam’iyyun siyasa, ofisoshin kungiyoyi, kamfanonin sayar da motoci, manyan shaguna, da wuraren kasuwanci da dama.
Wani mai shago a wata plaza da ke kan titin, mai suna Abubakar Ali, ya bayyana yadda wuraren zubar da shara a gefen titin suka lalata titin da aka san shi da tsafta a baya.

“Muna bukatar a jawo hankalin gwamnati, wannan wuri ya koma wajen zubar da shara. Kwantena na shara sun yi kadan kuma wadanda ke da alhakin kwashewa ba sa yin hakan a kai a kai. Wani lokaci sai bayan watanni suke zuwa su kwashe. Hakan na jawo sauro da wari, suna shafar harkokin kasuwancinmu matuka.”
Shi ma wani dan kasuwa Salisu Malan, ya bayyana irin wannan damuwa, inda ya ce kusan makonni bakwai ke nan da aka kwashe sharar da ke kusa da shagon, har yanzu ba su sake zuwa ba.
“A da ana kwashe wannan shara a duk ranar Asabar, sannan masu kwashewa sukan share wurin gaba daya. Amma yanzu kwantenan sun lalace saboda sakaci, kuma sun yi kadan. Wannan yanki ya kamata ya samu akalla kwantena biyar amma guda daya ne kawai, kuma duka jama’ar wurin ke amfani da shi. Hakan ya sa kwari sun mamaye wuraren kasuwancinmu,” In ji shi.
Ga Hamisu Abdullahi kuwa, babbar matsalar ita ce hadarin lafiya da tarin shara ke haifarwa, ganin yadda ake barinta na makonni ko watanni kafin a dauke.
“Wadannan wurare a da ba wurin zubar da shara ba ne, kwantena ne da ake kwashewa a kowane mako sannan a feshe da magunguna. Amma yanzu ba sa kwashewa, ba sa kuma fesin wuraren. Ba a Titin IBB kadai ba, ko’ina cikin gari haka yake.

“Wannan shara ta kunshi tarkace da dama, ruwan sama na turata cikin magudanan ruwa har cikin gidajen mutane. Hakan babban hadari ne ga lafiyar dan Adam, zai iya haddasa cututtuka da dama. Wani hadari kuma shi ne yadda ake amfani da wuraren zubar da shara wajen yin bayan gida a fili. Ya kamata gwamnati ta dauki mataki cikin gaggawa,” In ji Abdullahi.
Wadannan mazauna sun yi kira ga Gwamnan Katsina, Malam Dikko Radda, da ya dauki mataki ta hanyar umartar hukumomin da abin ya shafa, fa su kara samar da kwantena na shara, da kwandunan gefen hanya da wuraren kona shara a Titin IBB da sauran wuraren cikin garin Katsina.
Haka kuma sun bukaci Hukumar Kare Muhalli ta Jihar Katsina (SEPA) da ta aiwatar da aikinta yadda ya kamata wajen tabbatar da tsafta da lafiyar muhalli a duk fadin jihar.
Daga Isma’il Adamu
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
