Connect with us

Labarai

Gwamnatin Zamfara Ta Jajantawa Iyalan Wadanda Suka Mutu A Hatsarin Jirgin Ruwa

Published

on

Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana alhininta kan mummunan hatsarin jirgin ruwa da ya auku ranar Juma’a a Nasarawan Kifi, da ke Gundumar Birnin Tudu ta Karamar Hukumar Gummi, wanda ya yi sanadiyar mutuwar wasu mutane da ke kokarin tserewa daga harin ’yan bindiga.

A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na jihar, Mahmud Muhammad Dantawasa, ya fitar, ya ce rahotannin farko sun nuna cewa jirgin ruwan ya ɗauki fasinja ne fiye da ƙima, wanda hakan ya jawo kifewar sa a tsakiyar hanya, inda ya  haddasa asarar rayuka da dama.

Ya bayyana cewa ana ci gaba da aikin ceto da binciko wadanda suka bace, inda ƙungiyoyin gaggawa ke aiki tare da shugabannin al’umma domin tantance adadin mutanen da suka ɓace da kuma bayar da agajin gaggawa ga waɗanda suka tsira.

A madadin Gwamnatin Jihar Zamfara, muna mika ta’aziyyar mu ga iyalan waɗanda suka rasu, tare da roƙon Allah ya jikansu da rahama,” In ji sanarwar.

Mahmud Dantawasa ya ƙara da cewa gwamnatin jihar na aiki don ganin iyalan da abin ya shafa sun samu tallafi da agaji cikin gaggawa.

A cewarsa, Gwamna Dauda Lawal ya umurci jami’an tsaro da su ƙara kaimi wajen gudanar da ayyuka a yankin, domin hana ƙarin hare-haren ’yan bindiga da kuma kare rayukan mazauna ƙauyukan da abin ya shafa.

Ya sake tabbatar da aniyar gwamnatin Zamfara na kawo ƙarshen matsalar ’yan bindiga.

 

Daga Aminu Dalhatu

 

 

 

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara