Connect with us

Labarai

Jihar Jigawa Ta Zamto Jagora A Arewa Wajen Gyaran Tsarin Makamashi

Published

on

Jihar Jigawa ta samar da gagarumin ci gaba a fannin samar da makamashi, bayan da Gwamna Malam Umar Namadi ya kaddamar da aikin karamar tashar lantarki a Kafin Hausa, wanda shi ne na farko cikin shirin samar da megawatt 10 a fadin jihar.

An kaddamar da aikin ne a tashar samar da wuta ta Bagaja,  tare da layin rarraba wuta mai tsawon kilomita uku da rabi .

Gwamna Namadi ya bayyana aikin a matsayin mataki mai dinbin tarihi, yana mai cewa shi ne sakamakon yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin gwamnatin jihar da kamfanin samar da wuta na KEDCO, bayan jihar ta zuba jarin kashi 10 bisa 100 a kamfanin.

Ya ce shirin zai taimaka wajen magance matsalar karancin hasken wuta a Jigawa, tare da samar da makamashi ga manyan birane kamar Dutse, Hadejia, Kazaure, Ringim da Gumel.

Gwamnan ya danganta wannan ci gaba da Manufar Sabon Fata ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wadda ta bai wa jihohi damar samar da wutar lantarki.

Ya kuma bayyana cewa aikin ya yi daidai da manufofin gwamnatinsa 12, wanda ya fi mayar da hankali kan wutar lantarki mai, da samar wuta mai amfani da hanken rana a kauyuka da cibiyoyin gwamnati,  tare da ƙarfafa zuba jari daga masu zaman kansu.

Namadi ya jaddada matsayin Jigawa a matsayin jagora a Arewa wajen gyaran tsarin makamashi, inda ita ce jiha ta farko da ta kafa Ma’aikatar Makamashi da Wuta,  kuma ta farko da ta amince da Dokar Lantarki ta Jiha ta 2024.

Haka kuma, ya bayyana cewa jihar na shirin samar da megawatt 100 ta hanyar haɗin gwiwa da masu zaman kansu, baya ga aikin  samar da kananan tashoshin 21 da ake aiwatarwa a yankunan da ba su da layin wuta, a karkashin shirin samar da wutar lantarki na Nigerian Electrification Project (NEP).

Ya ce wadannan matakai za su kara samar da wutar lantarki a Jigawa, da bunkasa tattalin arzikin jihar, tare da inganta rayuwar jama’a.

 

Usman Muhammad Zaria 

Labarai

Ilimi1 day ago

KANO: Ungogo Ta Ƙaddamar da Shirin Shigar da Yara Makaranta

Daga Khadijah Aliyu Ƙaramar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano ta ƙaddamar da wani shirin wayar da kan jama’a domin shigar...

Labarai1 day ago

Jihar Naija Ta Dauki Matakan Gaggawa Sakamakon Bullar Cutar Ebola A Abuja

Daga Aliyu Lawal Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Nijar ta sanya Cibiyar Ayyukan Gaggawa ta Lafiyar Jama’a (PHEOC) cikin shirin ko-ta-kwana,...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya

Daga Bello Wakili  Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da matakan gaggawa na kare lafiyar jama’a,  bayan tabbatar da bullar cutar...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Fitar Da Naira Biliyan 1.4 Ga Mazabu

Daga Usman Muhammad  Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira biliyan 1.4 wajen aiwatar da ayyukan mazabu...

Fasaha2 days ago

Jigawa Ta Ware Naira Miliyan 380 Don Samar da Wutar Lantarki a Cibiyoyin ICT

Daga Usman Muhammad Zaria  Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira miliyan 380 wajen samarwa...

Labarai2 days ago

’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano

Daga ABDULLAHI JALALUDDEEN, KANO Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da aikata fashi da...

Labarai2 days ago

2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro

Daga ALIYU MURAKI, LAFIA Ɗan takara a zaɓen gwamnan Jihar Nasarawa na jam’iyyar PDP, Dr. Emmanuel Ombugadu, ya yi alƙawarin...

Labarai2 days ago

Tajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14

Daga BELLO WAKILI, Abuja Shugaban Majalisar Wakilai ta Najeriya, Dr. Abbas Tajudeen, ya ce zai bayyana cikakken rahoton nasarorin da...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga

Daga AMINU DALHATU Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana matuƙar damuwarta kan ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan jihar a...

Kasuwanci2 days ago

APC Ta Ce Kebbi Na Tare da Tinubu Dari-bisa-Dari

Daga SANI DUTSINMA Babban Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulazeez Yari, ya ce...

Mafi Shahara